An dora alhakin barkewar kwalara a kan 'ruwa mai tsarki' a Habasha

Wani marar lafiya a kwance a gadon asibiti

A kalla mutum 10 sun rasa rayukansu yayin da wasu fiye da 1, 200 ke kwance a asibiti bayan barkewar mummunar kwalara a kasar Habasha.

Ana dai yi wa wadanda suka kamu da cutar magani a wani asibiti da ke babban birnin yankin da cutar ta bulla wato Mekelle.

Mahukunta a kasar sun dora alhakin barkewar cutar da kuma yaduwarta a kan rashin tsaftataccen ruwan shan da mutanen garin ke amfani da shi da kuma wani gurbataccen ruwa da suke kira tsaftatacce da ake sha a wuraren ibda a yankin.

Mahukuntan sun ce ana debo ruwan ne a wani kogi maras tsafta don haka suke ganin kamar daga nan ne ake daukar cutar.

Tsoma baki a kan abubuwan da suka shafi addini a yankin abu ne mai wutar gaske, amma kuma duk da haka gwamnatin kasar na aiki tare da shugabannin addinin yankin domin hana amfani da wannan ruwa mai tsarki.

Yanzu haka dai an shawo kan yaduwar cutar, amma kuma duk da haka ana ci gaba da kokari wajen kawar da ita kwata-kwata.

Karanta wasu karin labaran