An gano makeken kabari da gawawwaki 166 a Mexico

Asalin hoton, Getty Images
An dade jami'an tsaro na yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi
An gano kwarangwal na akalla mutane 166 a wani makeke kabari a jihar Veracruz da ke gabashin Mexico.
Babban mai gabatar da kara na kasar Jorge Winckler ya ce an binne gawawwakin mutane sama da shekaru biyu.
Sai dai hukumomin kasar ba su bayyana inda aka gano makeken kabarin ba.
Masu fataucin miyagun kwayoyi sun dade suna amfani da yankin Veracruz a matsayin yankin da suke watsi da gawawwakin mutanen da suka fada tarkonsu.
An taba gano gawawwkin mutane 250 a wani makeken kabari a yankin.
Mista Winckler ya shaidawa manema labaria cewa an kuma samu tufafi da wasu kayayyaki sama da 200 da katin sheda na mutane sama da 100.
Hukumomi dai na gudanar da bincike kan kwarangwal da aka samu domin tantance mutanen da aka kashe.
Rikicin masu fataucin miyagun kwayoyi dai ya kara tsananta tun 2016 bayan tura jami'an tsaro domin yakarsu.
Sama da mutane 200,000 aka kashe a rikicin, yayin da alkalumman gwamnatin kasar suka ce sama da mutane 37,000 suka yi bata.
