An yi yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa

Jair Bolsonaro dan takarar zaben shugaban kasa a Brazil

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bidiyo ya nuna yadda aka daba wa dan takara Jair Bolsonaro wuka a wajen gangamin yakin nemansa zabensa

Wani dan takarar shugaban kasa mai cike da cece-kuce a Brazil ya tsallake rijiya da baya a wani hari da aka kai masa yayin gangamin yakin neman zabe a arewa maso gabashin kasar.

Wani mahari ne ya dabawa Jair Bolsonaro da ake wa lakabi da Trump din Brazil wuka a ciki, lokacin da ya ke yi wa dandazon magoya bayansa jawabi a birnin Juiz fora.

Maharin ya bula masa hanji da bangaren mararsa inda nan take aka ruga da shi zuwa asibiti.

Shugaba Micheal Temer ya yi allawadai da harin, yana mai cewa abu ne da ba za a amince da shi ba a kasar da take bin tsarin dimukradiyya.

"Mutane ba za su iya fita yakin neman zabe cikin kwanciyar hankali ba, a wajen kamfe mutane ke bayyanawa al'umma abin da za su yi musu amma kuma hakan na faruwa, abin takaici ne ga dimukradiyyar kasar nan," in ji shugaban.

Magoya bayansa sun ce an yunkurin halaka dan takararsu ne da ake ganin zai lashe zaben Brazil.

Likitoci sun ce yana cikin mummunan hali duk da ya farfado bayan nasarar tiyata cikin sa'o'I biyu da aka yi masa.

'Yan sanda sun ce sun cafke maharin nan take bayan da ya kai harin.

Mista Bolsonaro shi ne kan gaba a dukkanin kuri'un jin ra'ayin jama'a da aka gudanar gabanin zaben Brazil da za a gudanar a watan gobe.

Dansa Flavio ya ce kusan a matacce aka tafi da shi asibiti.

A lokacin da yake bayyana yadda lamarin ya faru ya ce "gaskiya ne an yi yunkuri halaka mahaifina, bidiyo ya nuna yadda wani ya daba masa wuka a zuciya. Allah ya sa akwai wani kusa da shi da ya yi gaggawar cire wukar a zuciyarsa."