Tasirin motsin kasa a Abuja

Yankunan da mostin kasar ya shafa a Abuja
Bayanan hoto,

Yankunan da mostin kasar ya shafa a Abuja

Akalla katangun gidaje 10 ne suka rushe a unguwar Mpape da ke wajen Abuja, sakamakon motsin kasa da ake fusknata a birnin cikin yan kwanakin nan.

Mazauna yankin sun ce lamarin ya tayar musu da hankali, ya firgita su, sannan a halin yanzu suna zaman dar-dar na rashin tabbashin mai zai faru gaba.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA tuni ta gargadi mazauna Abuja su dauki matakan kare kansu sakamakon motsin da kasar ke yi a birnin tun ranar Laraba.

Mazauna Abuja suna ba da rahotannin motsin kasa da jin wasu sautuka a sassan birnin da dama.

Lamarin ya fi kamari a yankunan Maitama da Mpape.

Sai dai, an ji motsin a wasu sassan kamar Gwarimpa da Asokoro da Katampe da Utako da ma wasu sassan birnin da dama.

Matakan Kariya

NEMA ta ce yawan fasa duwatsu da hakar ma'adanai na daga cikin dalilan da ka iya janyo motsin kasa.

To sai dai duk da haka hukumar ta NEMA ta ce kada mazauna Abuja su ta da hankulansu, domin da wuya a fuskanci girgizar kasa a Najeriya, tun da kasar ba ta cikin yankunan da ake fuskantar wannan matsala.

NEMA ta bayar da shawarwari kan matakan da mutane za su dauka yayin da kasar ke motsawa.

  • A nutsu, a guji ta da hankali
  • Idan mutum yana cikin gini to ya tafi daki mafi aminci da babu shirgi, sannan ya shiga karkashin tebur ya kuma rike shi da kyau. Kada mutum ya kusanci taga ko wani abu da zai iya faduwa.
  • Idan mutum yana waje kuwa, ya nemi fili, sannan kada ya tsaya kusa da gini, ko bishiya ko kuma turken wayar lantarki, ko kuma karkashin wayar.
  • Idan mutum yana mota, to ya rage gudu, ya nemi fili ya tsaya, sannan kada ya fita daga motar har sai kasar ta daina motsi.

Hukumar ta NEMA ta kuma ba da tabbashin cewa nan ba da jimawa ba za a daina fuskantar motsin kasar.

Bayanan hoto,

Matsin kasar ya shafi gidaje a Unguwar MPape ta marasa galihu da ke wajen birin Abuja.