Abin da ya sa muka zabi Tauraruwar Hikayata – Farfesa Malumfashi

Abin da ya sa muka zabi Tauraruwar Hikayata – Farfesa Malumfashi

Alkalan Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta BBC Hausa, wato Hikayata, sun bayyana labarin ''Ya Mace', a matsayin labarin da ya yi zarra cikin labarai sama da 300.

Wata malamar makarantar sakandire mai shekara 29 da haihuwa ce ta zama Tauraruwar Hikayata ta bana.

Safiyyah Jibril Abubakar ta lashe gasar ne da labarinta mai suna 'Ya Mace.