An yi zanga-zanga kan kwana 1000 da tsare el-Zakzaky

Wasu 'yan mazahabar Shi'a a Najeriya

Asalin hoton, WHATSAPP/SAMINU

Daruruwan mabiya mazahabar Shi'a a Najeriya sun gudanar da zanga-zangar lumana a Abuja babban birnin kasar, domin juyayin cika kwanaki dubu daya da kama jagoransu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da kuma ci gaba da tsare shi tare da iyalansa.

Masu zanga-zangar sun rike kwalaye da hotunan malamin.

BBC ta tattauna da wasu daga cikin masu zanga-zangar, inda Abdullahi Muhammad Musa ya ce:

"Babban makasudun fitowarsu don gudanar da zanga-zangar shi ne domin a sako mana malaminmu, yau kwana 1000 cir yana tsare a hannun gwamnati ga ciwukan da aka ji mi shi, gashi kuma tare da matarsa ba a ba su cikakkiyar kulawa alhali kuma kotu ta ce a sake shi."

Ya ci gaba da cewa, "So yanzu abin da muke so shi ne a sake shi tare da matarsa da kuma sauran 'yan mazahabar da ke tsare."

Abdullahi Muhammad ya ce "Tun bayan tsare jagoranmu, muna rayuwa ne cikin kunci, amma kuma duk da haka babu abin da aka fasa, don haka idan ma an yi mana haka ne don a hana mu wani abu a kasa, to babu abin da za mu fasa."

Masu zanga-zangar sun yi tattaki a tituna a birnin Abuja musamman a kusa da sakatariyar gwamnatin Tarayya domin nuna rashin jin dadinsu.

An dai kama malamin ne a birnin Zariya a shekarar 2015.

Sai dai malamin ya yi shekara biyu yana tsare ba tare an gurfanar da shi a gaban kuliya ba, in ban da a 'yan watannin baya da gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da kara a gaban kotu.

Gwamnatin dai na tsare da Sheikh Zakzaky tun a shekarar 2015 bayan an samu wani tashin hankali tsakanin magoya bayansa da sojojin kasar a garin Zaria, lamarin da ya kai ga mutuwar daruruwan mabiya Shi'a.

Karanta wasu karin labarin