Rakumin dawa ya raunata uwa da danta

Rakumin Dawa

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Lamarin ya faru ne a Afirka ta kudu.

Wata mata da danta na cikin halin rai kwa-kwai mutu kwa-kwai bayan wani Rakumin dawa ya kai musu hari a wani wajen adana namun daji a kasar Afirka ta Kudu.

Katty Williams da danta mai shekara uku Finn, iyalan wani masanin kimiyya ne dan kasar Birtaniya.

An garzaya da su asibiti bayan da Rakumin dawan ya far musu ta kuma ji musu munanan raunuka.

Mijin matar Sam William wanda ya ke aikin a wajen adana namun dajin, ya ce rakumin dawan na ganin matar ta sa da dansa a matsayin barazana, shi ya sa ta kai musu hari.

Mr William ya ce dawowarsa ke nan daga wajen atisaye sai ya hango rakumin dawan ya kai wa iyalan nasa harin, bai kuma yi wata-wata ba, ya kora ta cikin wajen da suke a ajiye.

Asalin hoton, FAMILY HANDOUT

Ya ce ya dau wannan lamari a matsayin tsautsayi, amma rakumar dawan ba dabba ce da ta ke cutar da mutane, itama ta fito neman diyarta 'yar kimanin wata biyu a duniya ne lamarin ya faru.

Yanzu haka dai Mrs William da danta suna samun sauki a asibiti.

Kuma tuni mai kula da gidan namun dajin ya ce nemi afuwar Mr William a kan abinda ya faru.

Karanta wasu karin labaran