Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka makon jiya
Zababbun hotunan abubuwan da suka faru a Afirka da 'yan Afirka a makon jiya.

Asalin hoton, AFP
Nan Kenya ne yayin wani wasan rakuma da aka yi a ranar Lahadi
Asalin hoton, AFP
Wadanda suka shiga gasar rakuman sun yi gudun kilomita 21 a arewacin Kenya.
Asalin hoton, EPA
Nan kuma wani wasan tsere ne ake yi a Liberia inda iyaye kan goya 'ya'yansu a baya su rinka tseren a cikin tabo wanda ruwan saman da aka yi mai karfin gaske ya haddasa a ranar Talata.
Asalin hoton, AFP
Wasu 'yan ci-rani ne ke tafiya a cikin wani daji da suka buya saboda gudun 'yan sanda a kusa da gabar ruwan Morocco ta Tangier.
Asalin hoton, EPA
Wannan mutum yana share jar dardumar da aka shimfida wa Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel gabanin ziyarar ta a fadar shugaban Najeriya da ke Abuja a baya-bayan nan
Asalin hoton, EPA
A ranar Larabar da ta wuce ne abubuwa suka tsaya cak a garin Aswan da ke kasar Masar saboda hazon da aka yi ya sa ba a ganin wurare sosai.
Asalin hoton, AFP
Motoci sun yi dogayen layuka a wajen gidan man Shell da ke Kenya a ranar Alhamis saboda karin haraji da aka yi a kan kudin man fetir.
Asalin hoton, Reuters
A ranar Talata ne manyan mutane suka halarci bikin rantsar da shugaban kasar Mali Ibrahim Boubakar Keita.
Asalin hoton, EPA
Wani ma'aikaci yana fentin bangon daya daga cikin hanyoyin karkashin ruwa na Suez Canal da ake yi a Isma'ila mai nisan kilomita 120 gabas da birnin Alkhahira a ranar 4 ga watan Satumba.
Asalin hoton, AFP
Wasu masu bauta 'yan addinin Hindu suna maci a garin Chatsworth d ake kusa da garin Durban a ranar 2 ga watan Satumba.
Asalin hoton, Getty Images
Wani dan tseren kekuna a Port Elizabeth da ke Afirka ta kudu a gasar cin kofin zakarun Ironman
Hotuna daga AFP,EPA, Getty Images da kuma Reuters