Masifa ce ta fada wa Salisu Yusuf – Nuhu Ribadu

Masifa ce ta fada wa Salisu Yusuf – Nuhu Ribadu

Shugaban kwamitin da'a na hukumar kwallon kafa ta Najeriya da ya binciki zargin cin hanci da ake yiwa kocin Najeriya, Salisu Yusuf, Mallam Nuhu Ribadu ya ce kaddara ce ta fadawa Salisu Yusuf, ya karbi cin hanci.

Malam Nuhu Ribadu wanda tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ne na Najeriya EFCC ya ce sun samu shaida kururu cewa, Salisu Yusuf ya karbi kudi.

Tsohon shugaban na EFCC ya ce ba a son ransu suka yankewa tsohon kocin na Najeriya hukuncin dakatarwa da biyan tara ba.

Ya ce abin takaici ne a ce an samu tsohin kociyan cikin karbar rashawa, saboda yadda ake ganin kimarsa a duniya.

Ribadu ya ce amma dole ne doka ta yi aikin a kan kowa, don haka ne ma suka rufe ido suka hukunta shi.