Yadda Safiya ta lashe dala 2,000 a gasar rubutu ta mata zalla
Yadda Safiya ta lashe dala 2,000 a gasar rubutu ta mata zalla
Alkalan Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta BBC Hausa ta mata zalla, wato Hikayata, sun bayyana labarin ''Ya Mace', a matsayin labarin da ya yi zarra cikin labarai sama da 300.
Wata malamar makarantar sakandire mai shekara 29 da haihuwa ce ta zama Tauraruwar Hikayata ta bana.
Safiyyah Jibril Abubakar ta lashe gasar ne da labarinta mai suna 'Ya Mace.