Ana ce-ce-ku-ce kan saya wa Buhari fom na takara

Matasa sun saya Buhari fom

Asalin hoton, APC

Batun saya wa shugaba Buhari fom na takarar zabe na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya, inda wasu ke cewa hakan ya saba wa dokar zaben kasar.

Ma'anar "Dan takara" da "mai neman takara" ne dai ya janyo ce-ce-ku-cen ta la'akari da abin da kundin dokar zabe ya fada game da bayar da tallafi.

Wata kungiyar matasa ce da ake kira Nigeria Ambassadors Consolidation Network ta lale Naira miliyan 45 ta saya wa Buhari fom na sake neman takarar zaben shugaban kasa.

Amma wani sharhi da Jaridar Thisday da ake wallafawa a kasar ta yi, ya ce sayen fom din na miliyoyin Naira ga wani dan takara, ya saba wa dokokin zaben kasar.

Jaridar kuma ta yi kira ga shugaban ya yi watsi da fom din da matasan suka saya ma sa.

Jaridar ta ambato wani sashe da tace na dokar zaben Najeriya ne da ke cewa; "ba a yadda wani ya ba da tallafi na sama da Naira miliyan daya ga wani dan takara ba.

Sai dai kuma Jam'iyyar APC da kuma kungiyar matasan duka sun kare kansu, inda suka ce alherin saya wa Buhari fom bai saba doka ba.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Jam'iyyar ta ce akwai bambanci tsakanin mai sha'awar takara da kuma dan takara a dokar zabe.

Kuma ta ce tsoro ne kawai na 'yan adawa musamman ganin gudunmuwa daga dubban 'yan Najeriya da suka hada kudi suka saya wa Buhari fom.

Kungiyar da ta saya wa Buhari fom din ta ce rashin fahimta ce aka yi wa kundin dokar zabe ta 2010 da aka yi kwaskwarima.

"Har yanzu Buhari ba dan takara ba ne, sai bayan ya cike fom kuma an tantance shi," in ji Barista Sanusi Musa shugaban kungiyar matasan.

Sai dai kuma wasu masana shari'a a Najeriyar na ganin wannan yunkuri ya saba wa doka.

Barista Bulama Bakarti na Jami'ar Bayero ya ce sashe na 91 a dokar zabe ya yi amfani ne da kalmar dan takara ba tare an fayyace ma'anar ba.

Ya ce Kundin zabe ya yi amfani da kalmar a wurare 180 ba tare da kuma kotunan kasar sun fassara ma'anar kalmar ba.

"Kamar yadda Najeriya ke bin tsarin Amurka, idan har mutum ya bayyana aniyar tsayawa takara, to sunansa dan takara," in ji shi.