Jawabin Obama yana sa dadin bacci - Trump

Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Barack Obama Obama ya caccaki shugaba Trump tare da zargin jam'iyyar Republican da yiwa dimukrdiyya hawan kawara.

Tsohon shugban na Amurka ya gabatar da jawabi ne gaban 'yan majalisun kasar a wurin yakin neman zaben tsakiyar wa'adin mulki.

Obama ya yi kalamai da ba a saba ji ba na caccakar shugaba Trump, inda ya ce Amuruka na cikin lokaci mai matukar muhimmanci kuma mai matukar hatsari.

Ya ce gwamnatin Mista Trump ta bata dangantaka tsakanin kasar da aminanta tare da fifita matsayin Rasha.

Tsohon shugaban kuma ya yi kira ga Amurka su fito su tabbar da sauyi a zaben watan Nuwamba

Sai dai kuma game da jawabin na Obama, shugaba Donald Trump ya jawabin na Obama ya sanya bingire wa da bacci.

"Jawabin yana da dadin sa mutum bacci." in ji Trump.

Jam'iyyar Democrat ta Obama dai na kokarin karbe ikon shugabancin majalisar dattawan Amurka da wakilai a zabukan da za a gudanar a watan Nuwamba amma sai Democrat ta samu rinjaen kujeru 23 a majalsiar wakilai, kujeru biyu kuma majalisar dattawa.