Buhari 'yana kama-karya', Shekarau ya bar PDP: Hotunan Nigeria wannan makon

Mun zabo muku hotunan wasu abubuwan da suka faru a Najeriya da 'yan Najeriya wannan makon.

Kashim Shettima

Asalin hoton, Facebook/ Kashim Shettima

Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya dukufa yana karanta wani littafi a wani kantin sayar da littafai a birnin Berlin na kasar Jamus bayan ya halarci wani taro kan yankin Tafkin Chadi ranar Talata.

Asalin hoton, Twitter/Tom Brake

Bayanan hoto,

...a ranar ne wani dan majalisar Birtaniya, Tom Brake, ya nemi a saki Leah Sharibu, wato dalibar garin Dapchi da ke ci gaba da kasancewa a hannun 'yan Boko Haram, a gaban ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar.

Asalin hoton, Kungiyar NCAN

Bayanan hoto,

Wata kungiya ta saya wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari fom din takarar shugaban kasa a zaben 2019 a kan naira miliyan 45 ranar Laraba.

Asalin hoton, @twitter/elrufai

Bayanan hoto,

Mahalarta taron marubuta da masu zane-zane na #Kabafest a ranar Alhamis, rana ta biyu da soma taron wanda aka yi a otal din SilverSand, Kaduna.

Asalin hoton, ATIKU MEDIA OFFICE

Bayanan hoto,

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar lokacin da ya je mayar da fom din neman takararsa a babban zaben 2019 a sakatariyar jam'iyyar PDP da ke Abuja ranar Alhamis.

Asalin hoton, @twitter/bashir ahmad

Bayanan hoto,

...ranar ce kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Najeriya bayan ziyarar aikin da ya kai China.

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Bayanan hoto,

Washegari mataimakin shugaban Najeirya Farfesa Yemi Osinbajo ya karbi bakuncin 'yan matan da suka lashe gasar fasaha wacce aka yi a birnin San Francisco na Amurka.

Asalin hoton, KANO STATE GOVERNMENT

Bayanan hoto,

Ranar Juma'a shugaban APC Adams Oshiomole da Gwamna Ganduje na Kano suka ziyarci tsohon gwamnan jihar Ibrahim Sekarau, wanda ya fice aga jam'iyyar PDP ya koma APC.

Bayanan hoto,

...ranar ce kuma Musulmi mabiya mazhabin Shi'a suka yi zanga-zangar cika kwana 1000 da kulle shugabansu Ibrahim El-Zakzaky. Sun ce gwamnatin Buhari tana kama-karya saboda kin sakin sa duk da umarnin kotu, ko da yake gwamnatin ta daukaka kara kuma ana ci gaba da shari'a.

Asalin hoton, SAFIYYAH JIBRIL ABUBAKAR

Bayanan hoto,

...kazalika da safiyar Juma'a ne Alkalan Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta BBC Hausa, wato Hikayata suka sanar da cewa Labarin Safiyyah Jibril Abubakar mai suna ''Ya Mace' ne ya lashe gasar ta bana