An yanke wa Musulmi 75 hukuncin kisa a Masar

Hundreds gather at cross section of two roads in Cairo in 2013

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Jami'an tsaro sun kashe daruruwan masu zanga-zanga a dandalin Rabaa al-Adawiya a 2013

Wata kotun Masar ta yanke hukunci kan mutum fiye da 700 da ke goyon bayan kungiyar 'yan Uwa Musulmi wacce ta yi zanga-zanga bayan an tumbuke tsohon shugaban kasar Mohammed Morsi daga mulki a 2013.

Kotun ta tabbatar da hukuncin kisan da aka yanke a mutum 75 da kuma daurin rai-da-rai kan mutum 47, cikin su har da shugabannin Musulmi.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce hukuncin "bai dace ba" kuma ya keta kundin tsarin mulkin Masar.

Tarzoma ta barke a dandalin Rabaa al-Adawiya da ke birnin Alkahira a 2013 inda jami'an tsaro suka kashe daruruwan mutane.

A farkon wannan shekarar, majalisar dokokin Masar ta bai wa sojoji kariya kan kisan da suka yi a wancan lokacin da ma kashe-kashen da aka yi tsakaninwatan Yulin 2013 zuwa watan Janairun 2016.

An zargi mutanen da aka yanke wa hukuncin da laifukan da suka shafi tsaro ciki har da tunzura jama'a su yi bore da kisa da kuma shirya zanga-zanga ba bisa doka ba.

A watan Yuli ne aka yanke wa mutum 75 hukuncin kisa sai dai ranar Asabar ne aka tabbatar da hukuncin, abin da ya kawo karshen shari'ar.

Fitattun 'yan siyasa da shugabannin kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da aka haramta na cikin mutanen da aka yanke wa hukuncin kisa, cikin su har da babban jagoranta, Mohammed Badie.

Kazalika, fitaccen dan jaridar nan mai daukar hotuna wanda ya lashe lambobin yabo Mahmoud Abu Zeid, wanda aka fi sani Shawkan, zai sha daurin shekara biyar a gidan yari.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Mahmoud Abu Zeid

An tsare shi ne lokacin da yake daukar hotunan masu zanga-zangar yayin da ake tarwatsa su. Ana sa ran za a samllame shi bayan ya kwashe shekara biyar yana zaman wakafi.

Sojoji da 'yan sandan kasar sun kama daruruwan masu zanga-zangar goyon bayan Morsi, wadda aka yi wata guda bayan babban hafsan sojin kasar na wancan lokacin Abdel Fatah al-Sisi ya tumbuke shi daga mulki.