Kun san abin da ya sa arewacin Nigeria ya fi kudanci fama da talauci?

Bayanan sauti

Kun san abin da ya sa arewacin Nigeria ya fi kudu talauci?

Latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraren cikakkiyar hira da Dr Zahumnam Dapel

Wani masanin tattalin arziki ya ce arewacin Najeriya ya fi kudancin kasar fama da matsanancin talauci ne saboda ba ya sa samun kudin shigar da ya kai na kudu.

Dr Zahumnam Dapel ya shaida wa BBC cewa "kudaden shigar da jihohin Lagos da Ribas suke samu a shekara sun fi wadanda jihohi 14 na arewacin kasar ke samu, don haka suna da damar da za su kashe su kan al'umominsu."

Masanin tattalin arzikin, wanda ya yi aiki a Amurka, ya kara da cewa yawan talakawa da ke ci gaba da haihuwa ba tare da samun abin da za su bai wa iyalansu ba a arewacin Najeriya ya taimaka wajen ta'azzara talaucin da yankin ke ciki.

A cewar sa, jami'o'in da ke kudancin kasar sun fi na arewacin kasar, yana mai cewa "daga shekarar 1989 jami'oi 12 ne a arewa yayin da kudu ke da 17, amma a 2017 akwai jami'o'i 58 a arewa yayin da kudanci ke da 102. Idan kana ba mutum ilimi za ka fitar da shi daga talauci."

Ya kara da cewa satar da wasu 'yan siyasa ke yi ta kara jefa arewacin Najeriya cikin matsanancin talauci.

Dr Zahumnam Dapel ya ce jarin da gwamnatin ke bai wa 'yan kasar da kuma ciyar da 'yan makarantu suna taimakawa wajen rage radadin talauci yana mai cewa amma hakan ba zai warware matsalar baki daya ba.

Ya ce dole gwamnati ta taimakawa al'uma da takin noma da inganta wutar lantarki da hanyoyin sufuri da sauran su kafin mutane su fita daga talauci.