Ahmed Musa ya bai wa mara da kunya a wasan Supers Eagles da Seychelles

Ahmed Musa

Tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta doke ta Seychelles da ci 3-0 a wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka fafatawar rukuni na biyar.

Eagles wadda ta ziyarci Seychelles ta fara cin kwallo ta hannun Ahmed Musa minti 15 da fara tamaula, sannan Chidozie Awaziem ya kara ta biyu tun kafin aje hutu.

Bayan da aka dawo ne Odion Igahalo ya ci na uku a bugun fenariti.

Daya wasan rukuni na biyar din tashi suka yi babu ci tsakanin Afirka ta Kudu da Libya.

Da wannan sakamakon Libya tana mataki na daya a kan teburi da maki hudu, sai Afirka ta Kudu ita ma da maki hudu, sannan Nigeria ta uku da maki uku sai Seychelles wadda bata da maki a matsayin ta karshe.

Super Eagles za ta karbi bakuncin Seychelles a ranar 22 ga watan Maris, 2019.

Za a buga gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekarar 2019 a Kamaru.