Buhari ya wanke shugaban ma’aikatansa Abba Kyari daga zargin rashawa

Abba Kyari Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY
Image caption Abba Kyari ya ce zai maka Punch a kotu

Fadar shugaban Najeriya ta wanke Malam Abba Kyari, shugaban ma'aikatan Shugaba Muhammadu Buhari daga zargin rashawa.Jaridar Punch da ake wallafawa a kasar ce ta buga labarin da ya ce Malam Abba Kyari ya karbi hanci na N29m domin ya bai wa wani mutum kwangilar sayo motocin da za a rika amfani da su a fadar shugaban kasar.Labarin ya ambato wani mutum ya ce shi dan uwan Abba Kyari ne yana yin zargin cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar ya yi alkawarin ba shi kwangilar sayo motoci 15 kirar Hilux.Sai dai a cewar Punch, Abba Kyari da wani mutum da yake masa aiki sun ha'inci dan uwan nasa inda suka hana shi kwangilar sannan basu mayar masa da kudinsa ba.Amma wata sanarwa da kakakin Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya aike wa manema labarai ranar Asabar ta karyata zargin sannan ta sha alwashin gurfanar da jaridar Punch a gaban kuliya.

"Abin da ya fi ba mu mamaki shi ne Punch ta yi gaban kanta wurin wallafa wadannan karairayi duk da cewa hukumar da ke kula da bayar da kwangila ta ce mutumin da shi ne ginshikin labarin ba ma'aikacinta ba ne."Tun da zabe ya kusa, wasu 'yan siyasa da abokansu da ke gidajen jarida na matsa lamba kan gwamnatin Buhari inda suke fito da labaran kanzon-kurege," in ji sanarwar.Fadar shugaban Najeriya ta ce babu yadda za a yi batun bayar da kwangilar ya zama gaskiya saboda ba ya cikin kasafin kudin shekarar 2016 da 2017.

Karin labarai da za su so ku karanta: