Idlib ya kusa komawa hannun gwamnatin Syria

Birnin Idlib a lokacin da 'yan tawayen suka kwace shi a hannun gwamnati a 2015

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Birnin Idlib a lokacin da 'yan tawayen suka kwace shi a hannun gwamnati a 2015

Syria da kawarta Rasha su kaddamar da shirin kwace yankin Idlib a cikin kwanaki masu zuwa, yayin da Kasar da babbar kawarta Rasha ke shirin afka wa yankin.

Yankin shi ne na karshe da ke karkashin ikon mayaka 'yan tawaye da suka kwace a shekarar 2015 a yunkurunsu na hambare gwamnatin shugaban Syria Bashar al Assad.

Yankin Idlib ne yanki na karshe da ke hannun 'yan tawayen Syria, kuma bana shekararsu bakwai kenan suna kokarin fatattakar shugaban kasar Bashir al-Assad daga mulki.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai mutum miliyan 2.9 a yankin na Idlib, wadanda suka hada da kananan yara miliyan daya.

Yankin na da iyaka da kasar Turkiyya daga arewa, kuma yana kusa da wata babbar hanya da ta tashi daga Aleppo da ke kudu zuwa Hama, zuwa Damascus babban birnin Syria, har zuwa birnin Latakia da ke yamma a gabar tekun bahar Rum.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Dakarun Syria na dab da kwace yankin daga hannun 'yan tawaye

Idan gwamnatin Syria ta kwace yankin daga hannun 'yan tawaye, za su kasance an tarwatsa su kuma karshen yakin ya zo kenan.

Masana na ganin afka wa yankin gaba daya da yaki na iya kawo mummunan sakamako musamman ga dubban daruruwan mazauna yankin da dama ke cikin wani mawuyacin hali.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin na iya tilastawa fiye da mutum 800,000 basin muhallansu, kuma lamarin na iya kazancewa idan Syria da kawayenta kamar Rasha suka aiwatar da shirinsu na kwato yankin cikin kwanaki masu zuwa.