Rikici ya barke a APC a jihar Yobe

Gwamna Ibrahim Geidam na jihar Yobe

Asalin hoton, YOBE STATE GOVERNMENT

Bayanan hoto,

Gwamna Ibrahim Geidam na jihar Yobe

Ana ce-ce-ku-ce a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya reshen jihar Yobe bayan da gwamnan jihar Ibrahim Geidam ya zabi Sakataren Jam'iyyar na kasa Alhaji Mai Mala Buni a zaman wanda zai gaje shi a matsayin gwamna.

Sai dai kuma wannan bai yi wa wasu jiga-jigan jam'iyyar dadi ba abin ya sa har suka rubuta koke zuwa ga uwar jam'iyyar ta kasa suna cewa hakan ya sa'ba wa matsayar da aka cimma ta gudanar da zaben fid da gwani.

Daya daga cikin masu adawa da matakin gwamnan, Yakubu Muhammad ya shaida wa BBC yadda suke kallon matakin gwamnan:

"Abin da ke faruwa a Yobe shi ne, mutum daya ne ya kulle kofa ya kuma zabi abin da yake so. Wannan shi ne gwamnan jihar Yobe Dr. Ibrahim Geidam."

Ya kara da cewa, "Tun da farko shi ne ya zabi dan takarar gwamna, wanda ya ke so ya gaje shi, sabanin abin da mutane suke so."

Ya kuma koka da matakin gwamnan: "Muna tunanin za a yi mana adalci, amma daga karshe bamu sami adalci ba."

Asalin hoton, @officialapcng

Bayanan hoto,

Mai Mala Buni

To sai dai shugaban jam'iyyar a jihar, Adamu Abdu Chilariye ya ce gwamnan Ibrahim Gaidam ya bayyana ra'ayinsa ne kawai don haka za a yi zaben fid da gwani.

"Gwamna Geidam bai hana kowa sayen fom yayi takara ba, amma ya bayyana ra'ayinsa ne akan Alhaji Mai Mala Buni domin yana ganin shi ne zai iya cigaba da ayyukan da ya yi a jihar Yobe."

Ya kuma bayyana cewa. "Duk dan takarar da ya ci zaben fid da gwani, to yana bayansa."