Shekarau 'ya mika wuya ga Ganduje'

Shekarau da Ganduje

Asalin hoton, KANO STATE GOVERNMENT

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi watsi da jar hula a yayin da tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau ya kai masa ziyara ranar Asabar, jim kadan bayan ya bayyana cewa ya koma jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Sanya jar hula alama ce ta yin biyayya ga sanata Rabi'u Kwankwaso, mutumin da suka raba gari da Gwamna Ganduje bayan sun yi shekara da shekaru suna harokokin siyasa tare.

Malam Shekarau, wanda ya ziyarci Gwamna Ganduje sanye da bakaken tufafi, ya taras da Gwamna Ganduje sanye da nasa bakaken tufafin, ciki har da bakar hula - ba ja ba - kamar yadda ya saba.

Ya ce ya fice daga jam'iyyar PDP mai hamayya ce saboda rashin adalcin da aka yi masa.

Gabanin fitar sa daga PDP, tsohon gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa kan matakin da PDP ta dauka na rusa shugabancin jam'iyyar na jihar Kano, kana aka maye gurbin sa da kwamotin rikon-kwarya mai mambobi bakwai.

A cikin mambobin, biyu ne kawai 'yan bangaren Malam Shekarau, yayin da biyar ke bangaren tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi'u Kwankwaso wanda bai dade da komawa jam'iyyar PDP ba.

Sai dai PDP ta musanta zargin da tsohon gwamnan jihar Kanon ya yi mata cewa rashin adalcinta ne ya sa shi ficewa daga cikin ta.

Mai magana da yawun shugaban jam'iyyar, Malam Shehu Yusuf Kura, ya shaida wa BBC cewa sun dauki matakin ne saboda sun samun labarin Malam Shekarau na shirin ficea daga cikin ta tun da Sanata Kwankwaso ya koma cikin ta.

Rayuwar Ibrahim Shekaraua takaice

  • An haife shi a birnin Kano a 1955
  • Ya zama shugaban shahararriyar makarantar sakandare ta Rumfa College
  • Ya zama babban sakatare a ma'aikatar ilimi da matasa
  • Shekarau ya yi gwamnan jihar Kano sau biyu a jere
  • Da shi aka kafa jam'iyyar APC
  • Ya fice daga APC zuwa PDP a 2014
  • Ya zama ministan Ilimi a gwamnatin Goodluck Jonathan

Asalin hoton, @twitter/Shekarau4NG2019

"Tun mako takwas zuwa tara da suka gabata mun san yana magana da APC, mun san "yana tattaunawa da gwamnan jihar Kano a kan mukamai da za a ba shi. An yi masa alkawarin kujerar sanata da ta mataimakin gwamna da kujerun kwamoshinoni idan ya koma APC," in ji shi.

Amma mai magana da yawun tsohon gwamnan, Sule Ya'u Sule, ya ce babu kanshin gaskiya a zargin, yana mai cewa Shekarau ya bar PDP ne saboda rashin adalcin da aka yi masa.

Masu sharhi dai na ganin komawar Ibrahim Shekarau, wanda ya dade yana sukar gwamnatin Muhammadu Buhari, ba za ta samar masa wata martaba ba.

Lokacin da ya koma PDP bayan an kafa APC da shi, tsohon gwamnan jihar ta Kano ya ce ya yi haka ne saboda ba a yi masa adalci ba.

Sai dai wasu na ganin ya dauki matakin ne domin biyan bukatar kashin kansa, zargin da ya sha musantawa.