An gano gawar mata da yara a wani gida

Police are seen at a property in Bedford, Perth after a group of people were found dead

Asalin hoton, EPA

'Yan sanda a Yammacin Australia sun ce sun gano gawar mutum biyar a wani gida da ke wajen birnin Perth.

Gawarwakin sun hada da na mata da kananan yara. Wani mataimakin kwamishinan 'yan sanda Paul Steele ya ce lamarin abin daure kai ne sannan ana nuna damuwa kan tsaron lafiya a yankin.

Ya kara da cewa jami'ansu ne suka gano gawarwakin a gidan da ke kan titin Coode na Bedford bayan wani mutum ya kai kara ofishin 'yan sanda.

An tsare mutumin, mai shekara fiye da ashirin, a ofishin 'yan sandan. Har yanzu ba a san ko mutanen da suka mutu na da alaka da juna ba.

Mr Steele ya ce gano gawarakin abin tayar da hankali ne, yana mai cewa hakan zai sa mutanen da ke yankin su rika zama cikin fargaba.

Ya kara da cewa an aike da jami'an da ke binciken kwayoyin halittar dan adam domin su gudanar da bincike dalla-dalla.

A watan Yuli, an tuhumi wani yari dan shekara 19 bisa zargin kisan jarirai biyu da mahaifiyarsu a yankin Ellenbrook da ke wajen Perth.