Sojojin Nigeria sun sake kwace garin Gudumbali daga Boko Haram

Soji

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kwace garin Gudumbali da ke jihar Borno a arewacin kasar bayan mayakan Boko Haram sun yi ikirarin sun mamaye shi.

'Yan Boko Haram sun ce sun kashe sojin kasar uku sannan suka lalata motoci masu sulke tara a arangamar da suka yi da sojin ranar Juma'a.

Ganau sun shaida wa kamfanonin dillancin labaran Reuters da AFP cewa an kashe wasu mutane lokacin arangamar, ko da yake har yanzu ba a san adadin mutanen da suka mutu ba.

Sai dai mai magana da yawun rundunar sojin kasa Texas Chukwu ya ce babu wanda aka kashe sanadin bata-kashin.

Wata sanarwa da ya aike wa manema labarai ta ce "an yi taho-mu-gama da masu tayar da kayar bayan ne lokacin da suka kai hari kan garin. Sai dai babu wanda ya mutu. Dakarunmu sun sake taruwa wuri guda kuma an dawo da zaman lafiya a yanki."

A watan Yuni ne 'yan gudun hijira suka koma garin na Gudumbali bayan rundunar sojin kasar ta ce ba ya fuskantar barazanar tsaro.

A farkon watan Satumba, jami'an tsaron Najeriya, ciki har da sojoji 48 ne suka mutu bayan mayakan Boko Haram sun kai hari a sansaninsu da ke Zari na jihar Borno.