Hotunan fadi-tashin Shekarau cikin wata biyu
Mun zabo muku wasu daga cikin hotunan abubuwan da suka faru da tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau na siyasarsa a baya-bayan nan.

Asalin hoton, @KWANKWASORM
Ranar 29 ga watan Yuli, Sanata Rabi'u Kwankwaso ya kai wa Malam Ibrahim Shekarau ziyara a gidansa da ke Abuja bayan Sanatan ya koma PDP daga APC
Asalin hoton, KANO GOVERNMENT
Ranar Juma'a, bakwai ga watan Satumba, shugaban APC, Adams Oshiomole da mai Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano sun kai masa ziyara inda suka nemi ya koma APC
Asalin hoton, @Shekarau4NG2019
Asabar, takwas ga watan Satumba, ya koma APC bayan an yi kwan-gaba kwan-baya
Asalin hoton, @Shekarau4NG2019
... a ranar ne ya kai ziyarar 'mubaya'a' wurin Gwamna Ganduje
Asalin hoton, @Shekarau4NG2019
Shekarau ya yi rijistar shiga APC ranar Lahadi a mazabarsa da ke birnin Kano