Shugaban kasar Moldova ya yi hatsarin mota

Maldova

Asalin hoton, @Liveuamap

Shugaban kasar Moldova Igor Dodon ya ji rauni bayan hatsarin motar da ya yi a arewa maso yammacin Chisinau, babban kasar.

Kafafen watsa labaran kasar sun ce hatsarin ya auku ne lokacin da wata babbar mota ta yi kokarin wuce wata motar inda ta kutsa kai cikin ayarin motocin shugaban kasar kusa da garin Straseni.

Daya daga cikin motocin da ke ayarin ta wuntsula. An kai Shugaba Dodon asibiti.

An ce raunukan da ya ji ba su da girma, ko da yake kafofin watsa labaran kasar sun ce mahaifiyarsa na cikin matsanancin hali.

Shugaban mai shekara 43 shi ne yake jagorancin kasar da ke cikin tsohuwar tarayyar Soviet tun watan Disambar 2016.

Hotunan da aka wallafa a shafukan zumunta ranar Lahadi da rana sun nuna motar ta lalace.

Hatsarin ya auku ne awowi kadan bayan firai ministan Abkhazia, Gennady Gagulia, ya mutu sakamakon hatsarin mota.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Mahaifiyar shugaban kasar na cikin mawuyacin hali

Asalin hoton, @Liveuamap