'Yan sanda za su fara daure 'yan siyasa a Kano

Babban sufeton 'yan sandan Najeriya Hakkin mallakar hoto FACEBOOK NPF
Image caption Rundunar 'yan sandan ta ce 'yan siyasa na son tayar da husuma

Rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke Najeriy ta ce za ta soma daure 'yan siyasar da ke amfani da kalaman batanci wajen cin mutuncin shugabanni ko junansu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Magaji Musa Majiya ne ya bayyana wa BBC hakan lokacin taron masu ruwa da tsaki kan tsaftace kalamai a gidajen rediyo.

A cewar sa, `yan siyasar - wadanda aka fi sani da sojojin-baka - suna karewa juna tanaji maimakon su rungumi salon siyasa ba-da-gaba ba.

"Magana ake ta siyasa yadda za ka baje hajarka ba tare da cin tumunci da zagin mutane ba. Haka ne ya sa muka soma taro da shugabannin kafafen watsa labarai da sojojin-baka da kuma hukumar da ke sa ido a kafafen watsa labara, wato NBC. Mun yi zube-ban-kwarya, don haka babu sani babu sabo ga duk wanda ya karya doka," in ji Majiya.

Sai dai wani dan siyasa, Malam Adamu Danjuma Wapa, ya ce 'yan sandan sun mayar da su tamkar karamar katanga mai dadin ketara.

"Bamu taba ji an ce mun fadi kalamai masu kyau ba, kullum sai dai a ce mun fadi kalamai marasa dadi. Za ka ga mahukunta ba a cewa sun yi laifi; idan ana so a samu mafita, yadda na kasa zai yi laifi a hukunta shi, dole a hukunta na sama," a cewaar dan siyasar.

Da ma dai 'yan Najeriya na kokawa kan yadda 'yan siyasa ke aike wa da sojojin-baka kafafen watsa labarai su rika cin mutuncin junan su.