'Yan bindiga sun kai hari kan babban kamfanin man fetur a Libya

Smoke rises form the headquarters of Libyan state oil firm National Oil Corporation (NOC) on 10 September 2018

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Hayakin da ke fitowa daga kamfanin man ya turnuke yankin

Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan hedikwatar babban kamfanin man fetur da ke Tripoli, babban birnin kasar Libya.

Jami'an tsaro mun yi taho-mu-gama da maharan a kamfanin da ke tsakiyar birnin, kuma ganau sun ce sun yi ta jin karar harbe-harben bindigogi da kuma fashewar abubuwa.

A makon jiya ne majalisar dinkin duniya ta bayar da sanarwar cewa kungiyoyin 'yan bindigar da ke fada da juna a babban binrin kasar su yi sulhu.

Gwamnatin da majalisar dinkin duniyar ke mara wa baya ce ke mulki a Tripoli.

Amma kungiyoyin masu tayar da kayar baya ne ke rike da akasarin kasar.

Wani ma'aikacin kamfanin man, wanda ya tsallake ta taga ya tsere daga ginin, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa uku daga cikin 'yan bindiga biyar sun yi ta harbi a cikin ginin inda suka samu mutane da dama.

Ganau sun gaya wa Reuters an fitar da shugaban kamfanin man, Mustafa Sanallah, daga ginin ba tare da samun ko da kwarzane ba.

Ma'aikatan ba da ceto sun isa wurin domin taimakawa mutanen da suka ji rauni.

Har yanzu babu tabbaci kan kungiyar da ta kai harin.