An tsare mutumin da ya ci abinci da abokiyar aikinsa a Saudiyya

Saudi

Ma'aikatar kwadagon Saudiyya ta ce ta kama wani dan kasar Masar ma'aikacin otal bayan an nuna shi a bidiyo yana cin abinci da abokiyar aikinsa wacce ta yi lullubi.

Bidiyon, wanda aka yada a shafukan sada zumunta, ya nuna mutanen biyu suna cin abinci a kan teburi daya sannan suna daga hannu suna nuna wa a kamarar da ke daukar hotonsu.

Wani bangare na bidiyon ya nuna mutumin yana bai wa abokiyar aikin nasa abinci a baki.

Sanarwar da ma'aikatar kwadago ta fitar ranar Lahadi ta ce ma'aikatan da ke bincike sun kai ziyara a otal din, wanda ba a bayyana sunan sa ba, a birnin Makkah sannan suka tsare dan kasar ta Masar bisa keta dokokin aikin Saudiyya.

Kazalika an sammaci masu otal din "saboda gaza bin ka'idojin daukar mata aiki."

Dokokin kasar sun bukaci a samar wa mata wurin da za su yi aiki ba tare da sun cakudu da maza ba, ko da yake ba ko wacce ma'aikata ba ce ke biyayya ga dokokin.