'Malalata ne ke yin tsarin iyali'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba John Magafuli ya ce mutanen da ba sa iya aiki tukur ne suke haifo 'ya'ya kadan.

Shugaban Tanzaniya John Magafuli ya yi kira ga ma'aurata a kasar su ta haifo 'ya'ya, yana mai cewa "ragwayen mutane" ne kawai ke kayyade iyali.

Wata kafar wasta labaran kasar mai suna Citizen ta rawaito Mista Magafuli yana cewa kayyade iyali ne ya janyo raguwar yawan al'umma a nahiyar Turai, da kuma matsalar karancin ma'aikata.

Yana magana ne a kauyen Mearu a gabashin Tanzaniya.

Citizen ta rawaito cewa Shugaba Magafuli yana wannan jawabi ne a gaban wakilin Hukumar Kula da Yawan Jama'a ta Majalisar Dinkin Duniya a Tanzaniya Jacqueline Mahon, da ministar lafiya Ummy Mwalimu.

A yayin jawabin da ya yi, wanda mafi yawan wadanda suka halarta manoma ne, Mista Magafuli ya ce:

"Masu tsarin iyali malalata ne. Suna tsoron cewa ba za su iya ciyar da 'ya'yansu ba", in ji shi.

Ya ce, "Ba sa son yin aiki tukuru domin ciyar da iyalansu. Don haka ne suke kayyade iyali, sai ka ga sun buge da haifo da daya ko biyu.

"Na je Turai da wasu wuraren daban, na ga illar tsarin iyali. A wasu kasashen ma fama suke yi da karancin haihuwa. Ba su da ma'aikata", a cewar Shugaba Magafuli.

To sai dai wani dan majalisa Cecil Mewambe ya soki kalaman na Magafuli, inda a majalisa ya bayyana cewa tsarin inshorar lafiyar kasar zai iya daukarn nauyin mutum hudu ne kawa daga kowane iyali.

Labarai masu alaka