Matashin da ya kirkiro kayan kimiyya
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Matashin da ya kirkiro wa 'yan makaranta kayan kimiyya

Ba lallai ne daukan darusan kimiyya ya zama abinda kowane dalibi ya ke so ba. To amma ka yi tunanin cewa kana zaune a aji ba kayan aiki, ba dakin gwaje-gwaje.

Abinda yake faruwa ke nan ga miliyoyin dalibai a fadin duniya.

To sai dai wani matashi mai kirkire-kirkirkire a Ghana yana son sauya hakan, ta hanyar samar da kayan kimiyya, da ba su wuce girman littafi da kuma tsadar littafi ba.

Wannan labari na daga cikin shirin BBC na masu Fasahar Kirkira wato BBC Innovators, wanda Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta dauki nauyi

Labarai masu alaka