Akwai yiwuwar cimma yarjejeniyar Brexit nan da Nuwamba

Michel Barnier has said a Brexit deal is possible within six to eight weeks. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Michel Barnier na ganin za a iya kammala komai naan da mako takwas mai zuwa

Babban jami'i mai shiga tsakani akan batun ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai ya ce ana iya kammala tattaunawa akan batun ficewar da aka shirya kammala wa zuwa watan Nuwamba.

Kalaman Mista Michel Barnier sun faranta wa gwamnatin Birtaniya zuciya, bayan da ya ce yana ganin za a iya cimma daidaito zuwa tsakiyar watan Nuwamba kafin wani taron koli na shugabannin Tarayyar ta Turai da zai gudana domin rattaba hannu kan yarjejeniyar.

Sauyin matsayar da Tarayyar Turai ta yi ba yana nufin za ta yi watsi da sharuddan da ta gindaya ba ne, amma tana sane da cewa firaiministar Birtaniya Theresa May na fuskantar matsin lamba ta siyasa a cikin gida.

Masu adawa da Misis Theresa May sun gargade ta cewa za ta iya fuskantar bore daga 'yan jam'iyyarta ta Conservatives idan ta cigaba da shirinta na kulla wata dangantaka mai kwari bayan ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai.

Tsohon ministan Brexit Steve Baker ya ce kimanin 'yan majalisa 80 za su juya wa shirin baya idan aka gabatar da shi a majalisar wakilai ta Commons a karshen wannan shekarar.

Birtaniya da Tarayyar Turai na fatan kammala yarjejeniyar rabuwarsu da kulla sabuwar dangantakar cinikayya kafin karshen watan Oktoba, lokacin da za a gudanar da wani taron koli kan batun.

Mista Barnier ya kuma ce abu ne mai muhimmanci idan Birtaniya da Tarayyar Turaisuka sami isasshen lokacin nazarin shawarwarin da ke gabansu kafin ficewar Birtaniya daga kungiyar kawo 29 ga watan Maris shekara ta 2019.

Amma wasu manyan 'yan majalisa masu goyon bayan ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai na karfafa wa Firaiministar gwuiwa - inda suke ce mata ta cigaba da aiwatar da shirin nata, amma akwai yiwuwar dukkan shirin nata ya watse idan Tarayyar Turai ta ki amincewa da shi.