Dakarun Rasha da na China da na Mongolia na rawar daji

Russia has intensified combat drills for its armed forces - despite the expense Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rasha ta tsananta rawar daji ga dakarunta duk da tsadar yin haka

Rasha ta fara wani gagarumin atisayen yaki wanda shi ne mafi girma tun bayan yakin cacar baki.

Sojojin Rasha kimanin 300,00 ne za su shiga wannan atisayen mai suna "Vostok-2018" da zai gudana a gabashin Siberia.

Ma'anar 'Vostok' ita ce gabas da Rashanci.

Kasar Sin ta aika da dakarunta 3,200 zuwa rawar dajin da Rasha ta lakaba wa suna Vostok-2018 tare da motocin sulke da jiragen yaki masu yawa.

Mongolia ma ta aika da wasu sojoji da kayan yaki zuwa wajen wannan atisayen.

Ma'aikatar tsaro ta Rasha ta ce tankunan yaki 36,00 da motoci masu sulke dauke da sojoji ne za su shiga wannan rawar dajin da zai gudana daga 11 zuwa 17 ga watan Satumba, inda ta ce jiragen yaki 1,000 ne za su rufa ma dakarun nata baya.

Shugaba Vladmir Putin ya mayar da zamanantar da rundunonin sojojin Rasha - wadanda suka hada da kirkirar sabbin makaman nukiliya - wani muhimmin aikin gwamnatinsa.

An kiyasta cewa Rasha na da dakarun soji da auka kai miliyan daya.

Wannan rawar dajin zai kasance wata dama ga Rasha ta nuna karfin sojinta ga duniya, a daidai lokacin da kasar ke neman karfafa karfin fada aji a tsakanin manyan kasashen duniya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sojojin China da Rasha a yain wani atisayen da suka yi a bara

Sanin kowa ne cewa kasashen yammacin Turai na kallon Rasha a matsayin mai neman tada zaune tsaye, amma ta daya bangaren Rasha ma na kallon kungiyar NATO a matsayin wani babban kutse da ake ma ta a gabashin Turai.

Wannan matakin na nuni karara cewa Rasha ba za ta bari a sha gabanta ba wajen fuskar tsaro da karfin tattalin arziki.

Labarai masu alaka