Yunwa 'na karuwa a duniya'

Relatives mourn the death of an infant, who died as a result of malnutrition (Getty Images) Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wani rahoto da majalisar dinkin duniya ta fitar ya ce adadin mutanen da ke fama da yunwa ya karu cikin shekara uku da suka wuce.

Kididdigar da majalisar ta yi ta nuna cewa ya zuwa shekarar 2017, mutum 821m na fama da tamowa - wato mutum daya ke nan cikin mutane tara.

Kazalika, yara 'yan kasa da shekara biyar 151m ne ba sa girma yadda ya kamata saboda rashin abinci mai gina jiki.

Masu binciken sun ce matsalar sauyin yanayin da ake fama da ita a duniya na cikin dalilan da suka sanya karuwar masu fama da yunwa inda suka yi kira a auki matakan gaggawa na rage matsalar.

Rahoton, wanda aka yi wa take Halin da rashin abinci mai gina jiki ya jefa duniya a ciki, ya kara da cewa wahalar da ake sha kafin a samu abinci mai gina jiki ta taimakawa wurin samun mutane masu teba, inda cikin kowanne mutum takwas ake samun mutum guda da ke fama da matsalar yawan teba - wato mutum 672 m ke nan.

Wadanda suk fitar da rahoton sun ce abubuwan da ke haifar da sauyin yanayi - irin su ambaliyar ruwa, da fari da tsawa - sun nunka tun daga farkon shekarun 1990.

Sun ce: "rahoton ya ake da sakn da ke nuna girman matsalar sauyin yanayi da kuma illar da hakan ke haifarwa, kana ya nuna irin koma-bayan da aka samu wajenkawo karshen yunwa da rashin abinci mai gina jiki."

Labarai masu alaka