Ana bude iyakar Ethiopia da Eritrea

Daga hagu shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki da kuma Firai Ministan Ethiopia Abiy Ahmed lokacin da suka hadu don bude babbar hanyar kan iyakar. Hakkin mallakar hoto Ethiopia Government
Image caption (Daga hagu) Shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki da kuma Firai Ministan Ethiopia Abiy Ahmed lokacin da suka hadu don bude babbar hanyar kan iyakar.

Ranar Talata ake bude babbar hanyar iyakar Ethiopia da Eritrea bayan shekara 20 da rufe ta, sakamakon yakin da ya faru tsakanin su.

Shugabannin kasashen biyu suna daga cikin manyan bakin da suka halacci bude babbar hanyar kan iyakar a Burre, wanda hakan na daya daga cikin hanyar samun maslaha a tsakanin su.

Wannan zai ba wa 'yan Ethiopia damar zuwa tashar jiragen ruwa ta Assab.

Za a sake bude wata hanyar iyakar da ta hada kasashen biyu da ke kusa da garin Zalambessa a Ethiopia.

Bude hanyar iyakar ta ya faru ne bayan a watan Yuli firai Ministan Ethiopia Abiy Ahmed da shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki sun sa hannu a wata yarjejeniyar dawo da zaman lafiya da yin saye da sayarwa a tsakanin su.

Bikin bude babbar hanyar da ta hada kasashen biyu ya zo daidai da lokacin da Ethiopia ke bikin murnar shiga sabuwar shekara.

A watan Mayu 1998 kasashen biyu sun yi yaki inda kowacen su ke cewa hanyar iyakar na bangaren kasar ta kuma hakan ya jawo mutuwar dubban mutane.

Yakin ya kare ne a shekarar 2000 bayan kasashen biyu sun kulla yarjejeniyar kawo karshen fadan.

Iyalan da suka rabu saboda fadan za su samu damar zuwa su ga sauran 'yan uwansu bayan shekaru da rabuwa.

Eritrea ta kwaci 'yancin kanta daga wurin Ethiopia a shekarar 1991.

Labarai masu alaka