An mika wa Buhari fom din takara

Buhari Hakkin mallakar hoto Nigeria presidency

Kungiyar matasan Najeriya da ta saya wa shugaban kasar Muhmmadu Buhari fom din takara a kan N45m ta mika masa shi ranar Talata.

Da yake mika masa fom din a fadar shugaban kasa da ke Abuja, shugaban kungiyar Nigeria Ambassadors Consolidation Network Barista Sanusi Musa ya ce sun ji dadi da shugaban ya amince su saya masa fom din.

A cewar sa, sun sayi fom din ne domin sun gamsu da ayyukan da Shugaba Buhari ke yi na ci gaban Najeriya.

Ya yi watsi da sukar da wasu ke yi cewa bai kamata shugaban ya karbi fom din da wasu suka saya masa ba idan har da gaske yake yi a yakin da yake yi da cin hanci da rashawa.

Kungiyar ta saya wa shugaban fom din ne ranar biyar ga watan Satumba jim kadan bayan jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta fitar da kudaden da masu neman takara a jam'iyyar za su sayi fom.

Fom din shugaban kasa ne ya fi kowanne tsada, da ake sayar da shi a kan Naira miliyan 45.

'Bai dace ba'

To sai dai abin da mutane da dama ke mamaki shi ne yadda matasan suka sami miliyoyin kudin da suka saya wa Buhari fom din.

Bugu da kari hakan ya faru ne a daidai lokacin da wasu 'yan uwansu matasa ke korafin cewa kudin da jam'iyyar ta sanya ya yi musu tsada.

Akwai masu ra'ayin cewa matasan na rawa ne da bazar wasu manyan 'yan siyasa da suka ba su kudin sayen fom din, don a nuna cewa har yanzu Buhari yana da farin jini a wajen matasan kasar.

To sai dai shugaban kungiyar ta Nigeria Ambassadors Consolidation Network ya ce ko kadan ba bu wani jami'in gwamnati da ya basu kudi.

"Bari in yi rantsuwa, Wallahi tallahi babu wani jami'in gwamnati da ya ba da ko kwabo a kudin da muka biya," in ji Sanusi Musa.

Ya kara da cewa, matasan sun kai shekara guda suna tara kudi domin saya wa shugaban fom.

"Mutum daya ne, wani dan kasuwa dan kabilar Ibo kadai ya kawo mana gudunmuwar Naira miliyan biyar, da ya ji abin da muke shirin yi," in ji shi.

A cewarsa sun gamsu da irin shugabancin Buhari, don haka ne suka yanke hukuncin mara masa baya a zaben da ke tafe.

A zaben shekarar 2015 ma Muhammadu Buhari ya samu gudunmuwa daga 'yan kasar da dama wajen saya masa fom din takara da kuma kudin yakin neman zabe.

Sai dai wasu suna ganin da wuya a wannan karon ya samu irin wannan gudunmawar, kasancewar wasu 'yan kasar sun dawo daga rakiyarsa.

Wannan tunanin da wasu 'yan kasar ke yi na daga dalilan da Sanusi Musa ya bayyana cewa suka saya wa Buhari fom din, domin nuna wa jama'a cewa har yanzu matasa suna goyon bayan Buhari.

A shekarar 2014 dai kwamitin yakin neman zaben Shugaba Buhari ya fitar da wani kati wanda jama'a za su iya amfani da shi wajen ba wa Buhari gudunmuwa.

To sai dai babu tabbas ko a wannan karon ma za a yi amfani da wannan hanyar.

Kuma idan ma za a yi din shin jama'a za su bayar da gudunmuwa irin yadda suka bayar a baya?

Hakkin mallakar hoto NCAN
Image caption Matasan sun ce sun gamsu da mulki Buhari.