'Ana kashe mutum 57 kullum a Afrika ta Kudu'

Afrika ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ministan 'yan sanda Bheki Cele ya ce 'yan sanda dole su kara kokari

Ministan 'yan sanda Afirka ta kudu Bheki Cele ya ce kasar ta shaida mutuwar mutane 20,336 a bara, wanda kari ne idan aka kwatanta da irin lokacin a baya.

Cikin fushi ministan ya ce "hakan yana nufin ana kisan kai 57 a kowacce rana kamar ana yaki."

Bayanan 'yan sanda sun nuna cewa yawan kisan kai ya karu a cikin shekaru shida da suka gabata.

Francois Beukman, wanda ke jagorantar kwamiti na kula da 'yan sanda a majalisa dokokin kasar, ya bayyana yawan kisan a matsayin abin tsoro.

Ya yi kira ga 'yan kasar Afrika ta Kudu da kada su dauki hakan a matsayin al'ada mai kyau. "Dole ku gyara kasarku," in ji shi.

Ya yi alkawarin yin aiki tukuru don canja yanayin. Ya ce dole a warware wannan lamarin.

Ana alakanta yawan aikata kashe-kashen da ayyukan 'yan daba.

Labarai masu alaka