Gwamnan Fayose zai mika kansa ga hukumar EFCC

Ayodele Fayose Hakkin mallakar hoto TWITTER/FAYOSE

Gwamnan jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya, Ayodele Fayose, ya ce da zarar ya sauka dsaga mulki zai mika kan sa ga hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ta kasar, EFCC.

EFCC na zargin gwamnan da sace wasu kudade na jihar.

Ranar 15 ga atan Oktoba ne Gwamna Fayose zai sauka daga mulki bayan ya kammala wa'adinsa na biyu - ba a jere ba- na shugabancin jihar.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Talata da yamma, ya ce "jiya na mika wasika ga EFCC inda na shaida mata bukatata ta mika kai na a gare ta ranar Talata 16 ga watan Oktoba da misalin karfe daya na rana domin na yi bayani kan wasu batutuwa ko na amsa tambayoyin da nake da masaniya a kansu."

Mr Fayose, na jam'iyyar PDP, ya shahara wurin caccakar gwamnatin Shugaba Buhari bisa rashin iya tafiyar da mulki.

A watan Yuli ne dan takarar da yake goyon baya a zaben gwamnan jihar, wanda shi ne mataimakinsa, ya sha kaye a hannun Mr Kayode Fayemi, tsohon gwamnan jihar.

Da ma dai lokacin da mataimakin Fayose ya fadi zaben gwamnan jihar Ekiti, EFCC ta wallafa wani rubutu a shafinta na Twitter inda ta sha alwashin gudanar da bincike a kan Mr Fayose da zarar ya sauka daga mulki.

Sai dai hukumar ta sha suka daga wasu 'yan Najeriya kan hakan inda suka zarge ta da nuna rashin iya gudanar da aiki.