An soma aiki da dokar da ta haramta auren dole a Morocco

Matan Morocco Hakkin mallakar hoto AFP

An soma aiki da wata sabuwar doka a Morocco wacce ta haramta cin zarafin mata.

An fara aiki da dokar - wacce kuma ta haramta auren dole - ne bayan korafe-korafen da aka rika yi a shekarun baya-bayan nan kan cin zarafin mata.

Wani bincike ya nuna cewa ana cin zaafin mace shida cikin kowacce mace goma.

Yawaitar fyade a kasar ya ja hankulan masu amfani da hafukan sada zumnta na zamani.

'Yan kasar sun yi maraba da wannan doka, ko da yake wasu sun soke ta saboda ba ta fayyace abin da ake nufi da cin zarafi a cikin gida da kuma yi wa mata masu aure fyade ba.

Labarai masu alaka