'Dan Najeriyar da ke yin 419 daga gidan yari'

Lokacin da 'yan sandan New South Wales su ka saki shugaban gungun 'yan damfara da ake zargi. Hakkin mallakar hoto NSW Police
Image caption Lokacin da 'yan sandan New South Wales su ka saki shugaban gungun 'yan damfarar da ake zargi.

'Yan sandan Australia sun kama wani dan Najeriya da ke damfara daga cikin cibiyar tsaro ta shige da fice a birnin Sydney.

'Yan sanda a New South Wales sun ce mutumin mai shekara 43 shi ne shugaban masu tura sakonnin bogi inda su ke nuna cewa daga wani babban kamfani a ke turo sakon.

An kama wasu mutan uku da a ke zargi da laifukan, ciki har da satar takaddun shaida da yin zamba a soyayya.

Hukumomi sun ce gungun 'yan damfarar da a ke zargi sun sami sama da dalar Australiya miliyan 3.

Sufurtanda Arthur Katsogiannis ya ce an tura wa wasu mutane a Najeriya kudin kuma zai yi wuya a gano kudin.

A na zargin cewa an yi damfarar ne ta hanyar amfani da wayoyi 16 da katunan waya 17 duk a cikin cibiyar tsaro ta shige da fice ta Villawood da ke birnin Sydney.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Cibiyar tsaro ta shige da fice ta Villawood da ke birnin Sydney

An kama wani mutum mai shekaru 20 da kuma wasu mata, daya mai shekara 20 da kuma mai shekara 36 a Sydney.

Sufurtanda Katsogiannis ya ce 'yan sandan Australia da hukumomin tsaro na duniya zasu ci gaba da bincike don gano inda kudin yake.

Ya bukaci kamfanoni da su inganta tsaron shafukansu na intanet, sannan su yi hankali wajen tura kudi.

  • Cibiyar tsaro ta Villawood babban wuri ne da zai iya daukar mutane 600.

Wani rahoto da Hukumar kare hakkin bil adama ta Australiya ya nuna, cibiyar na dauke da mutane 450 daga sama da kasashe 60 a watan Afrilun bara. Da yawansu ba su da takardun izinin shiga kasar wato biza, ko kuma takardun nasu ba su cika ba ko kuma su na neman mafaka, a cewar rahoton.