Limamai sun biya kudin gyara mutum-mutumin marigayi Lenin

Lenin statue in Shahritus, Tajikistan, 2013 Hakkin mallakar hoto Yuen Kim/YouTube
Image caption Shahritus Lenin a shekarun baya kafin a kayar da shi

Kafofin yada labarai a yankin tsakiyar Asiya na bayar da rahotannin da ke cewa wasu malaman addinin Musulunci a kudancin Tajikistan sun biya kudin gyara wani mutum-mutumin marigayi Lenin, wanda shi ne ya jagoranci kafa tsohuwar tarayyar Sobiyet.

Marigayin ne kuma ya jagoranci juyin juya halin da ya kawo mulkin kwamunisanci, wanda ya kuma kakaba wa kasar shekara 70 ta mulkin da ba a amince da wanzuwar ubangiji ba a kasar.

Limaman da suka fito daga garin Sharitus sun yi amfani da kudaden da masallata kan tara a masallatan garin wajen biyan kudin gyarawa da mayar da mutum-mutumin akan dandamalin da aka ture shi shekara biyu da ta gabata, kamar yadda tashar rediyo ta Radio Ozodi ta bayana a wani rahoto.

Bayan mayar da shi kan mazauninsa na ainihi, an kuma shafa masa fenti mai launin zinare, sannan an mayar da hannunsa daya da ya balle.

Mehriniso Rajabova ta majalisar gudanarwa a garin Shahritus ta ce limaman ne suka kawo shawarar yin wannan aikin da kashin kansu.

Ta fada wa gidan rediyon Ozodi cewa, "Sun shafa wa mutum-mutumin fenti, kana suka tsaftace filin shakatawa da ke zagaye da wurin, har ma sun gyara famfo mai wasa da ruwa".

Daya daga cikin limaman da yayi magana da gidan rediyon na Ozodi ya ki bayyana yawan kudin da suka kashe, amma ya ce kowane masallaci ya bayar da gudunmawar dalar Amurka 100 na sadaka da masallata ke tarawa a kowane mako.

Hakkin mallakar hoto Radio Ozodi
Image caption Hoton mutum-mutumin na Lenin na mika sabon hannun nasa da aka gyara

An kafa mutum-mutumin na Lenin tun lokacin mulkin tsohuwar tarayyar Sobiyet ne a 1980, kuma shi ne mafi girma da tsayi a yankin kudancin Tajikistan.

Bayan samun 'yanci da shekara 11, an rusa yawancin mutum-mutumin wannan shugaban da ya kasance uba ga tarayyar ta Sobiyet.

Amma an kyale wannan na garin Sharitus saboda yana da muhimmanci a bangaren tarihin kasar.

Amma a shekarar 2016, mahukuntan kasar sun rika maye gurbin mutum-mutumi na shugabannin tsohuwar tarayyar Sobiyet da na shugabannin Tajikistan da suka riga mu gidan gaskiya.

A lokacin ne suka aika da mutum-mutumin Lenin din zuwa kauyen Obshoron, inda aka adana shi a wani filin da magina kan ajiye kayansu.

'Tarihinmu'

Limamn ba su bayyana dalilinsu na biyan kudin gyaran mutum-mutumin na Lenin ba, amma dandamalin da aka ciro shi ya kasance fayau, kuma babu komai a madadinsa na fiye da shekara biyu.

Martani

Wannan lamarin dai ya ja hanukulan mutane a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama ke bayana al'ajabinsu. "Ai wadannan ba limamai bane, masu bautar gumaka ne," inji wani mutum bayan da ya bayyana ra'ayinsa a shafin intanet na gidan rediyo Ozodi.

Wasu kuwa cewa su kayi kamata yayi da an yi amfani da kudin wajen "taimaka wa marasa galihu".

Amma wasu kuma kamanta halin da kasar Tajikistan ta ke a yau da yadda aka rika rayuwa a zamanin mulkin tsohuwar tarayyar Sobiyet.

Sun ce "Limaman sun yi daidai. Da ba dun Lenin ba, da dukkan al'umomin yankin tsakiyar Asiya sun kasance jahilai kamar yadda lamarin yake a Afghanistan". inji wani mai suna 'Muhojir'.

Akwai wadanda suka ce babu laifi a yi waiwaye don tunawa da tarihin kasar. "Ko jagoranmu ne ko ba jagoranmu ba ne, wannan ne gaskiyar tarihinmu, kuma ya dace 'ya'yanmu su san tarihin kasarsu," kamar yadda wani ya bayyana a shafin intanet na gidan rediyo Ozodi.

Hakkin mallakar hoto DIMITRI BORKO/AFP/Getty Images
Image caption A karshen zamanin mulkin tarayyar Sobiyet, an sauke yawancin mutum-mutumin Lenin da ke Tajikistan