Yadda matsalar fyade take addabar al'ummar Kaduna

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Cibiyar Salama na tallafa wa wadanda aka ci zarafinsu ta hanyoyi daban-daban

Lokacin da na tambaye ta abin da ya faru da ita, kafin kiftawa da bisimilla, sai ta fara karkarwa, bakinta ya rika rawa kamar wadda ruwan sama ya yiwa dukan tsiya, idanuwanta suka yi jajir, suka cika da kwalla.

A cikin dan kankanin lokaci duk ta bi ta sauya kamar ba ita ba ce 'yan dakikoki kadan kafin wannan lokacin ta ke murmushi.

Asabe (ba asalin sunanta ke nan ba) matar aure ce mai kimanin shekara 20 da haihuwa wadda ke zaman jin dadi da farin ciki da mijinta.

Kamar yadda ta saba, a wata rana daga cikin ranaku ta kama hanya cikin jin dadi da annashuwa ta nufi gona — abin da ba ta sani ba shi ne a wannan rana rayuwarta za ta sauya, sama za ta koma kasa.

A wannan rana aka bi ta har gona aka yi mata fyade — abin da har yau ba ta iya bude baki ta yi magana a kai.

Akwai mata da 'yanmata da dama wadanda suka shiga irin yanayin da Asabe ta shiga, kuma sakamakon haka suka kidime suka shiga wani mugun hali; kamar yadda hukumomi a jihar Kaduna ta arewacin Najeriya suka nuna, yawansu karuwa yake yi.

Sai dai ba dukkan su ne suke samun taimakon shawarwari a kan yadda rayuwarsu za ta koma daidai bayan abin da ya same su ba, kamar yadda Asabe ke samu.

Cibiyar Salama

Asabe na samun wannan tallafi ne dai a wata cibiya inda ake baiwa wadanda tsautsayi ya fada kansu kulawa mai suna Salama Sexual Assault Referral Centre da ke Babban Asibitin Gwamna Awon a unguwar Kakuri ta cikin birnin Kaduna.

Cibiyar na da likitanta na musamman, da malamar jinya da lauya wadanda ke aiki ba dare ba rana don tallafa wa wadanda aka ci wa zarafi ta hanyar fyade.

Ginin cibiyar dai karamin waje ne, inda aka rarraba shi daki-daki, kama daga dakin duba marar lafiya, da dakin bayar da shawarwari sai kuma daki na musamman mai dauke da kayan wasan yara wanda shi kuma daki ne inda a ke kwantar wa da yaran da a ke kai wa cibiyar hankali.

Mene ne fyade?

Dakta Nu'uman Habib, masanin halayyar dan Adam ne a Jami'ar Bayero da ke Kano kuma a cewarsa, "fyade ya na nufin haike wa mata, wani sa'in ma har maza ba tare da izininsu ba, ba tare da sahalewarsu ba, ba tare da yardarsu ba."

Dakta Nu'uman ya ce tasirin fyade na da girma musamman a rayuwar yara, don kuwa ya kan dade a kwakwalwarsu kuma ya jefa su cikin damuwa da tsoro da rashin yarda da amincewa.

"Duk wanda su ka hadu da shi sai su yi tsammanin mai irin wannan halayyar ne. Kuma damuwar ta kan dade tare da su a cikin kwakwalawarsu kusan ta sa ma su sukurkuce", a cewar sa.

Sai dai bisa alama jama'a basu gane haka ba, don kuwa ba a cika tattauna batutuwan da su ka shafi fyade ba, bare a bai wa wanda a ka yi wa taimakon da ya dace. Hasali ma, idan a ka yi wa wata ko wani fyade, shi da iyalansa su kan zage dantse su tabbatar mutane ba su sani ba. Wannan ba ya rasa nasaba da kyama da ake nuna wa wadanda aka yi wa fyade da iyalen su.

Kuma wannan yana hana jami'an tsaro yin aikinsu yadda ya kamata, musamman ta fannin bincike da yanke hukunci ga wanda ya aikata laifin.

'Na yi bakin ciki matuka'

Wata mahaifiya ta shaida min cewa ta ji bakin cikin da bata taba jin irinsa ba a rayuwarta lokacin da aka yi wa 'yarta mai shekara biyar fyade, a hanyarta ta zuwa makaranta.

"Na yi bakin ciki matuka, a ranar in zauna in ci abinci ma ya gagareni. Saboda ganin yarinyata karama ce a ka aikata mata wannan abu." In ji mahaifiyar.

Shi kuwa wani mahaifi da a ka yi wa 'yarsa mai shekara 7 fyade ya shaida wa BBC cewa, bakin cikin da ya tsinci kansa a ciki ba zai misaltu ba.

Kuma a cewarsa da ya je gurin 'yan sanda ko sa share masa hawaye sai su ka watsama masa kasa a ido.

"Idan ba ka da kudi, 'yan sanda ba za su yi maka kallon mutunci ba, duk abunda za su yi sai ka ba su kudi" a cewarsa.

Ya ce kudin da ya kashe a wajen 'yan sanda ya kai kusan Naira dubu talatin, bayan an kama wanda ake zargi da yi wa 'yar sa fyade.

Ya ce "Shi yaron da aka kamo shi, da aka je aka ajiye shi sai da na rika bayar da kudin da zai dinga cin abinci safe da yamma, kwana bakwai ina ciyar da shi."

Matsayin Jami'an tsaro

Image caption Iyaye na zargin 'yan sanda da kin daukar mataki yadda ya kamata

Sai dai 'yan sanda sun musanta wannan zargi, na cewa ba sa aikinsu yadda ya kamata.

DSP Aliyu Muktar, tsohon kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar Kaduna, ya bayyana cewa rashin bai wa jami'an tsaro hadin kai da iyayen yaran da a ka yi wa fyade ke yi, shi ne babban kalubalen da rundunarsa ke fuskanta.

Ya ce "Mafi yawancin matsalar da a ke samu daga 'yan uwa ko iyayen wadanda aka yi wa fyaden ne."

"Lokuta da dama idan ana binciken laifi na fyade su suke matsa mana lamba su ce a daina maganar, wani lokaci ma su kan bayar da kudi don kawai a bar maganar."

Wani lokaci, 'yan uwan wanda ya aikata laifin ne za su tattauna da 'yan uwan wanda aka yi wa fyade su yi yi yarjejeniya a tsakaninsu, daga baya sai su matsa wa 'yan sanda kan su kashe maganar, wai don a ganinsu idan a ka ci gaba da bincike aka yanke hukunci, sunan 'ya'yansu zai baci a gari, kamar yadda DSP Mukhtar ya bayyana.

Rawar shugabannin al'umma

Image caption Masarautu na taka muhimmiyar rawa wajen yaki da fyade a unguwanni

A al'adance idan aka samu afkuwar irin wadannan laifuffuka na fyade a al'umma, a matakin fari a kan je ne ga iyayen al'umma kamar sarakuna ko hakimai ko dagatai ko kuma masu unguwa.

Alhaji shehu Tijjani, Barden Kudun Zazzau kuma hakimin gundumar Makera a jihar Kaduna ya bayyana min cewa su ma a bangarensu, su na ganin karuwar fyade a unguwanni.

Ya ce shaye-shaye a tsakanin matasa na daya daga cikin abubuwan da ke janyo yawaitar fyade. Ya kuma yi gargadin cewa iyaye su rika kula da mutanen da su ke kawowa gidajensu a matsayin 'yan aiki domin su ma su na bata yara kanana.

Kyama

Image caption Wata rijiya da aka jefa gawar wata yarinya da a ka yi wa fyade

Kyama ta kasance babban jigo a batutuwan da su ka shafi fyade. Sau da yawa, a kan kyamaci wanda aka yi wa fyade, babu mamaki saboda addini da al'ada da suka haramta mace ta tara da wanda ba mijinta ba. Ko kuma saboda ta na iya samun juna biyu ya kasance ta haihu ba tare da aure ba, ko kuma saboda cututtuka da ake iya dauka ta hanyar jima'i.

Kyamar da ake nuna wa wadanda aka yi wa fyade ya sa iyaye da dama ba sa fitowa fili su fadi idan a ka yi wa 'ya'yansu fyade. Hatta manya da a ka yi wa fyade, ba kasafai su ke fadi ba ballantana su kai kara ga hukumomi.

Wannan matsala ta sa ba a iya daukar matakai a kan wadanda su ka aikata laifukan fyade, kuma hakan na taimaka wa wajen yaduwar matsalar, kamar dai yadda DSP Aliyu Mukhtar ya fadi.

Ita ma lauya ta musamman a cibiyar Salama Barrister Jamila Sama'ila, ta bayyana cewa babban kalubalen da ta ke fuskanta a aikinta yana kasancewa ne daga bangaren iyaye ko kuma su wadanda a ka yi wa fyaden da kansu.

A cewarta, "wasu lokuta iyayen wanda a ka yi wa fyade ne da kansu za su kawo kara, amma da zarar bincike ya yi nisa sai su ce suna so a janye maganar kwata-kwata. Sai wasu iyayen maza su ce idan mahaifiyar ta ci gaba da zaman kotu, zai sake ta."

Kyama ta zama babban kalubale wajen yin adalci ga wadanda aka yi wa fyade.

A wata unguwa a cikin garin Kaduna, na hadu da wani mahaifi da a ka yi wa 'yarsa fyade, wanda ya yi mata fyaden ya karya mata wuya sannan ya jefa gawarta a cikin wata tsohuwar rijiya.

Sai dai mahaifin ya shaida min cewa bai kai karar wanda ake zargi da aikata laifin ba, duk kuwa da cewa ya san shi kuma dan uwansa ne na jini.

Dalilinsa- mahaifiyarsa ta ce ya bar maganar kar ya kai ta gaba ga hukuma, saboda yin hakan na iya bata zumunci a tsakanin danginsu.

Uwa mabada mama

Cibiyar Salama dai ta zama uwa ma ba da mama ga wadanda aka yi wa fyade.

Ta kuma zama abin koyi, don kuwa saboda nasarorin da ta samu wajen tallafawa wanda a ka ci zarafinsu, a yanzu gwamnatin jihar Kaduna ta shirya bude wasu cibiyoyin tallafa wa wadanda a ka yi wa fyade guda 3 a wasu sassa na jihar.

Baya ga kula ta lafiyar jiki da a ke bai wa wadanda aka ci zarafinsu, akwai mai bayar da shawarwari ga wadanda aka yi wa fyaden da ma iyayensu idan kananan yara ne.

Rhoda Agai, ita ce mai bayar da shawarwarin da kwantar wa da yara kanana hankali idan an kawo su cibiyar cikin yanayi na dimuwa bayan an yi musu fyade.

Ta shaida min cewa bayar da shawarwari na taka muhimmiyar rawa wajen sauya rayuwar wadanda aka yi wa fyaden.

Ta ce sau da yawa iyayen wadanda a ka ci wa zarafi su kan fi 'ya'yan nasu shiga mummunan hali, saboda abin da ya faru da su, amma a cewarta "da zarar na kwantar musu da hankali da dadadan kalamai, na tabbatar musu da cewa rayuwar 'ya'yansu ba ta lalace gaba daya ba, sai ki ga hankalinsu ya kwanta."

Bayar da shawarwari a cibiyar na tafiya ne hannu da hannu da kulawar lafiya da likita ke bayarwa ga wadanda a ka yi wa fyade.

Likitan ya bayyana min cewa yana bayar da magungunan ciwon jiki, da na rage radadi amma wani lokaci a kan kawo wasu da sai an yi musu dinki ko kuma sai an yi tiyata.

Daurin rai da rai ga masu fyade

Hakkin mallakar hoto Twitter/Hafsat Baba
Image caption Ana fata dokar kare hakkin yaran za taimaka wajen kawo karshen matsalar fyade a jihar Kaduna

Hajiya Hafsat Baba, ita ce kwamishiniyar kula da harkokin mata da ci gaban al'umma a jihar Kaduna kuma ta shaida min irin hankoron da gwamnatin jihar ta hanyar hukumarta ke yi don kare yara.

Cikin ayyukan da ta ke yi, gwamnatin jihar ta sa hannu kan wata doka wacce ta tanadi daurin rai da rai ga duk wanda aka samu da laifin cin zarafin kananan yara ta hanyar fyade.

Hajiya hafsat ta bayyana cewa a baya, idan aka kama mutum da laifin fyade a kan ci tara ne kawai amma yanzu tana fata wannan dokar za ta kawo sauyi.

Ta kuma ce dole ne iyaye su san illar sake a kan 'ya'yansu don kuwa dokar na da tanadi ga iyayen da ba sa bai wa 'ya'yansu kula yadda ya kamata.

Labarai masu alaka