Shin za a gurfanar da Kemi Adeosun gaban shari’a?

Kemi Hakkin mallakar hoto NIGERIA FINANCE MINISTRY

Wasu 'yan Najeriya sun yi kira a hukunta tsohuwar ministar kudi Mrs Kemi Adeosun bisa laifin yin jabun takardar hidimar kasa.

Ranar Juma'a ne shugaban kasar Muhammadu Buhari ya amince da saukar ministar daga kan mukaminta, fiye da wata biyu bayan jaridar Premium Times ta wallafa labarin da bankado cewa  Mrs Adeosun ba ta yi hidimar kasa ba.

Dokar Najeriya dai ta tilasta duk mutumin da ya yi karatu zuwa matsayin digiri kuma bai kai shekara 30 ya yi hidimar kasa ta shekara daya.

Sai dai labarin da jaridar ta wallafa ya nuna cewa tsohuwar ministar kudin, wacce aka haifa a Burtaniya sannan ta yi karatunta a can, ba ta yi hidimar kasa ba.

Hasalima, jaridar ta ce Mrs Adeosun ta mallaki takardar da ake bai wa wadanda suka kai shekara 30 amma ta jabu.

'A daure ta'

Dokar NYSC ta tanaji hukuncin daurin shekara daya ko tarar N2000 ko duka ga duk mutumin da ya ki yin hidimar kasa idan bai wuce shekara 30 ba.

Jam'iyyar PDP mai hamayya a kasar ta bukaci Shugaba Buhari ya sa a kama tsohuwar ministar sannan a hukunta ta.

Wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar ta ce ya kamata a gudanar da bincike kan ma'aikatar kudi saboda zargin da aka yi cewa wasu sun rika amfani raunin da tsohuwar ministar ke da shi wajen karbar makudan kudade a hannunta.

Wani fitaccen mai sharhi, Farfesa Farooq Kperogi, ya yi kira a hukunta ministar.

"Kada mu manta cewa Kemi Adeosun ta yi jabun takardun hidimar kasa wanda babban laifi ne da zai sa a daure duk dan Najeriya da ya aikata."

Tsohuwar ministar dai ta ce ba ta san takardar hidimar kasar da aka ba ta ta jabu ba ce, yana mai cewa babu yadda za ta sani tun da ba a Najeriya aka haife ta kuma ta girma ba.

Hakkin mallakar hoto NIGERIA FINANCE MINISTRY

Sai dai wani fitaccen mai amfani da shafukan sada zumunta, Bhadmus Hakeem, ya ce bai ga dalilin da zai sa ministar ta ce bata san laifi ba ne karbar takardar da ake bai wa mutanen da suka wuce shekara 30 ta hidimar kasa ba domin kuwa ba ta kai shekarun ba lokacin da ta kammala digirinta.