Wacece sabuwar ministar kudin Nigeria?

Mrs Zainab Shamsuna Ahmed Hakkin mallakar hoto Twitter/@ZainabAhmedS

Shugaban Najeriya Muhammafdu Buhari ya nada Mrs Zainab Shamsuna Ahmed a matsayin mai rikon mukamin ministar kudin kasar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Mr Femi Adesina ya fitar ya ce Mrs Ahmed za ta soma aiki ne ranar Juma'a, 14 ga watan Oktoba.

An nada a kan mukamin ne bayan saukar Mrs Kemi Adeosun sakamakon zargin yin cogen takardar hidimar kasa.

Mrs Ahmed ce karamar minista a ma'aikatar kasafin kudin kasar gabanin nadin nata.

Tarihin Zainab Ahmed a takaice

  • An haife ta a 1960 a jihar Kaduna
  • Ta yi digiri na daya a Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria.
  • Ta yi digiri na biyu a Jami'ar jiha ta Ogun da ke Ago-Iwoye
  • Ta shafe fiye da shekara 28 tana aiki a fannin harkokin kudi
  • Ta shugabanci hukumar Nigerian Extractive Industries Transparency Initiative, NEITI.
  • Ita ce karamar minista a ma'aikatar kasafin kudi