Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 100 a Nigeria

Ambaliya Hakkin mallakar hoto Nema

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta ce fiye da mutum 100 suka mutu a kasar sanadiyar ambaliyar ruwa cikin mako biyu.

Shugaban hukumar, Injiniya Mustapha Maihaja ne ya shaida wa BBC wannan labari.

A cewar sa, "Girman ambaliyar ruwan ya isa, shi ya sa muka samu kan mu a halin da muke ciki; saboda daga lokacin da abin ya soma tsakanin sati biyu an rasa mutum sama da 100. A Naija kadai an rasa mutum 41."

Ya kara da cewa ambaliyar ruwan ta fi ta'azzara a jihohi 12, wadanda suka hada da Kebbi da Kwara da Naija da Kogi da Benue da Adamawa da Taraba da Bayelsa da Edo da Anambra da Rivers da Delta.

Injiniya Maihaja ya ce idan kogunan Naija da Benue suka ci gaba da yin ambaliya za a ayyana dokar ta-baci kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci a yi.

Sai dai ya ce hukumarsa ta kai agajin gaggawa ga sassa daban-daban da lamarin ya shafa.

Wasu dai na zargin hukumar da karkatar da tallafin, ko da yake shugaban na NEMA ya ce a baya ne aka yi haka amma yanzu sun yi wa tufka hanci.

Image caption Ambaliyar ta lalata dukiya mai dimbin yawa a Jibiya a watan Yuli

Ga karin labarai:

Labarai masu alaka