Kaciya ta sa an kwantar da mata 50 a asibiti

Masu fafutuka Hakkin mallakar hoto AFP

An kwantar da mata kusan 50 a asibiti a Burkina Faso bayan an samu tangarda a kaciyar da aka yi musu, in ji sashen Afrique na BBC.

Wasu daga cikin matan ba su wuce shekaa hudu a duniya ba. An kama mata biyu 'yan kimanin shekara 60 da iyayen wasu matan da aka yi wa kaciyar kan batun.

An haramta yi wa mata kaciya a Burkina Faso tun 1996, kuma wadanda aka samu laifin yin kaciyar ka iya shan daurin shekara uku a gudan yari.

Ministar harkokin mata, Laurence Marshall Ilboudo, ta ce matan da aka yi wa kaciyar sun fi wadanda aka ba da labari yawa, sai dai ba a gano wasun su ba.

An yi wa matan kaciya ne tsakanin hudu zuwa shida ga watan Satumba a yankin Kaya, mai nisan kusan kilomita 100 daga babban birnin kasar, Ouagadougou, in ji ministar.

An kwantar da wasu daga cikin matan a asibitin lardi na Kaya Regional sannan aka kwantar da 38 daga cikin su a asibitin Chiphra Protestant da ke Ouagadougou.

Wani likita mai suna Dr Dieudonne Ouedraogo ya ce wasu daga cikin matan sun samu manyan raunuka.

Labarai masu alaka