Amurka ta saka wa China takunkumin $200bn

A shipping container is lifted at a rail port on August 18, 2018 in Erenhot, Inner Mongolia Autonomous Region of China. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Amurka na kara fadada takunkumain da ta ke sanyawa China

Amurka ta kakaba wasu sabbin takunkumai na dalar Amurka biliyan 200 akan kayayyakin China a yayin da ta ke fadada yakin cinikinta da kasar.

Kari mafi yawa zai shafi haraji kan kayayyaki fiye da 5,000, wanda shi ne mafi girma kawo yanzu.

Kayan da karin ya shafa sun hada da jakunkunar hannu, shinkafa da yadudduka, amma an cire agogogunan zamani da kayan rubutu.

China ta sha alwashin mayar da martani idan Amurka ta dauki wannan matakin.

Sabbin harajin za su fara aiki daga 24 ga wannan watan na Satumba, inda za su fara da kashi 10 cikin 100, kana su tashi zuwa kashi 25 cikin 100 a farkon shekara mai zuwa.

Shugaba Trump ya ce wadannan jerin takunkuman sun biyo bayan halayyar China ne na "rashin adalci a cinikayya, da suka hada da bai wa kamfanonin kasar tallafi a wasu sassa na kasar".

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption China ta saka wa Amurka nata jerin harajin kan kayan da kasar ke shigarwa kamar motoci da babura

Amma yawancin kamfanonin Amurka ba su goyi bayan wannan matakin na shugaba Trump ba.

Manoma da masana'antu masu kere-kere da manyan kamfanoni sun shiga wata hadaka da ke adawa da karin harajin, domin sun ce suna karewa kan 'iyalan Amurkawa ne.

Martanin da China ta dauka kawo yanzu

China ta kakaba wa Amurka takunkumi na dalar Amurka biiyan 50 a baya, a fannin kayan noma, wanda shi ne ya fi damun magoya bayan shugaban na Amurka.

Gwamnatin China ta kuma shirya saka wa wasu kayayyakin Amurkan harajin dala biliya 60, sannan ta na da shirin fadada shi.