Dan Kenya ne ya lashe Gasar Komla Dumor ta BBC ta 2018

Mr Mwaura sanannen dan jarida ne a kasar Kenya.

Waihiga Mwaura Hakkin mallakar hoto Joshua Wanyama
Image caption Mr Mwaura fitaccen dan jarida ne a Kenya

Wani dan jarida mai kuma gabatar da shiri a talbijin dan kasar Kenya ne ya lashe gasar Komla Dumor ta BBC ta shekarar 2018.

Waihiga Mwaura shi ne ke gabatar da shirin labarai wanda aka fi kallo a tashar talbijin ta Citizen.

Daga cikin garabasar da zai samua nasarar da ya yi, zai shafe wata uku a BBC a Landan, daga bisani sai ya koma nahiyarsa ta Afirka don ya yi rahoto kan wani labari a wajen.

An bayar da kyautar don girmama Komla Dumor, wani mai gabatar da labarai a BBC World News, wanda ya yi mutuwar farat daya yana dan shekara 41 a shekarar 2014.

Mista Mwaura shi ne na hudu da ya taba cin kyautar, bayan da 'yar Uganda Nancy Kacungira ta lashe lambar yabo ta shekarar 2015, sannan 'yan Nijeriya Didi Akinyelure da Amina Yuguda suka biyo baya.

Shi sanannen dan jarida ne wanda ake girmamawa a fadin Kenya, wanda ke rahotonni a kan wasanni da siyasa.

Ya ce: "Komla Dumor yana nufin abubuwa masu yawa a gare ni a matsayin dan jarida kuma a matsayin mutum," in ji shi.

"Idan zan iya samun ko da kashi 10 ko 20 cikin 100 na abin da ya yi, ina jin kamar zan yi taimako mai yawa a aikin jarida.

"A matsayina na dan Afirka, ina alfaharin samun damar da zan iya ba da labarin Afirka ga masu sauraro a fadin duniya."

Ya burge alkalan gasar da basirarsa ta bayar da labari da yadda yake gabatar da shiri a talbijin.

Alkalan sun ce kaunarsa ta son bayar da labari mai kyau game da Afirka da binciken kwakwaf a aikin jarida ne ya sa ya yi wa sauran wadanda suka shiga gasar zarra.

Labarai masu alaka