Yadda sojojin Kamaru suka 'hallaka' mata da yara
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Bidiyon yadda sojojin Kamaru suka hallaka mata da yara

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A watan Yulin 2018 ne wani bidiyo mai daga hankali ya fara yaduwa a shafukan sada zumunta.

Ya nuna yadda wasu sojoji suka tisa keyar wasu mata biyu da kananan yara biyu a gaba da bindiga.

An rufe idon mutanen, aka dankwafar da su kasa, sannan aka harbe su sau 22. Gwamnatin Kamaru ta yi watsi da bidiyon tana mai cewa 'labarin kanzon kurege ne'.

Amma binciken kwaf da sashen BBC Afirka ya gudanar, ta hanyar yin sharhin bidiyon dalla-dalla, ka iya nuna ainihin abun da ya faru, da lokacin da ya faru, da kuma wadanda suka yi kisan.

Labarai masu alaka