Buhari ne dan takarar shugaban kasa na APC a 2019

Shugaba Buhari da mataimakinsa Osinbajo
Image caption Jam'iyyar APC ta tsaida Buhari ba tare da hamayya ba

Jam'iyyar APC mai mulki a Nigeria ta sake tsayar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin dan takararta a zaben shekara mai zuwa, da za a yi a watan Janairu.

Wannan na zuwa ne sa'o'i kadan bayan ministar mata Aisha Jummai Alhassan ta sanar da yin murabus tare da ficewa daga jam'iyyar APC.

Ita ce ta biyu cikin ministocin gwamnatin shugaba Buhari da ta fice daga jam'iyyar bayan kin tantance su a matsayin 'yan takarar gwamna a jihohinsu.

Neman wa'adin shugabanci na biyu na Buhari ne ya tilastawa wasu 'yan jam'iyyar APC sauya sheka zuwa jam'iyyun adawa.

Zaben wanda aka gudanar bisa tsarin kai-tsaye da ake kira kato bayan kato, rahotanni sun ce shugaban ya samu kuri'u miliyan biyu da dubu dari tara a jihar Kano.

Kawo yanzu babbar jam'iyyar adawa ta PDP ba ta fidda wanda za ta tsayar dan takarar shugaban kasa ba, da zai kalubalanci shugaba Buhari.

Rikicin cikin gida ya dabaibaye jam'iyyar APC mai mulki a matakin jihohi, inda aka samu rarrabuwar kawuna tsakanin wasu gwamnoni da mataimakansu.

Misali rikici tsakanin gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari da mataimakinsa Malam Ibrahim Wakkala bayan gwamnan ya tsaida dan takarar da ya ke son ya gaje shi.

An kara samun wasu 'yan takara da ake kira G8 a Zamfara da suma suka samu matsalar da ta janyo suka dare gida biyu.

Wasu dai na ganin zaben fitar da gwani da aka dauki salon wakilai, zai iya kawo son rai saboda zargin wakilan na iya zaben wanda gwamna ke so ya gaje shi.

Wasu na ganin zaben kato bayan kato shi ya fi cancanta, domin ba al'umma damar su zabi abin da suke so ba wani ya zaba musu ba.