Shin APC na iya hade kan 'ya'yanta bayan fidda 'yan takara?

Gwamnan Legas Ambode Hakkin mallakar hoto Getty Images

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta yi zaben fitar da 'yan takara na gwamnonin jihohin Bauchi da Legas da Zamfara wadanda aka dage zuwa Litinin.

Dukkanin jihohin guda uku na fama da rikicin cikin gida na jam'iyyar APC tsakanin masu hamayyar neman kujerar gwamna.

A jihar Bauchi 'yan jam'iyyar za su sake fitowa ne domin zaben fidda gwani bayan da zaben ya ci tura a ranar Lahadi.

Uwar jam'iyyar ta kasa ce ta dage zaben, bayan da wakilanta da za su yi zaben suka kasa isa jihar a kan lokaci.

'Yan takara hudu ne ke hammaya a Bauchi da suka hada da gwamnan jihar mai ci Muhammad Abdullahi Abubakar da tsohon ministan'yan sanda Ibrahim Yakubu Lame.

Sauran sun hada tsohon ministan lafiya Muhammadu Ali Pate da kuma wani tsohon jami'in jam'iyyar na kasa, Muhammad Bala Jibrin wadanda ke neman takarar gwamna a APC.

Wasu daga cikin 'yan takarar dai sun bayyana jin dadinsu da matakin dage zaben zuwa Litinin.

Malam Nasiru Ibrahim Darazo mai magana da yawun mai neman takara Ibrahim Yakubu Lame ya shaidawa BBC cewa sun san cewa dole a dage zaben saboda jinkirin kawo kayan aiki da kuma jami'an zaben tare shan alwashin za su kayar da gwamna mai ci.

Sai dai kuma Kwamaret SaboMuhammad mai bai wa gwamnan jihar shawara kan wayar da kan jama'a ya ce masu hamayyar za su sha kunya a zaben.

Za a dai yi amfani ne da tsarin 'yar tinke ne domin zaben dan takarar gwamnan a jihar Bauchi.

Zaben dan takarar APC a Zamfara

Hakkin mallakar hoto @AhmedRufaiI
Image caption Gwamnan Zamfara da mataimakinsa sun yi hannun-riga

A Zamfara ma a ranar litinin ne ake sa ran za a yi zaben fidda-gwani a tsakanin masu neman takarar gwamnan na jam`iyyar APC a jihar da ke arewacin kasar.

Akalla mutum shida ne za su fafata a zaben.

Hedikwatar jam`iyyar APC ta kasa ce ta dage zaben zuwa Litinin, sakamakon jinkirin da aka samu wajen isar jami`an zabe da kuma kayan aiki jihar.

`Yan jam`iyyar APC a jihar ta Zamfara sun shafe wunin Lahadi suna tsammanin isar `yan kwamitin zabe a daidai lokacin da ake gudanar da zaben fidda gwanin a wasu jihohi makwabta.

Wasu daga ciki sun ce za su ci gaba da jira sai sun ga abin da ya hana tulu gashi.

Za a yi amfani da tsarin zabe ne na `yar tinke a jihar kamar yadda aka tsara.

Tun da farko adadin masu neman takarar ya kai kusan mutum goma.

Amma yanzu akalla mutum shida ne za su jarraba farin-jininsu a zaben, sakamakon janyewar da wasu daga cikin masu neman takarar suka yi, ciki har da mataimakin gwamnan jihar, Mallam Ibrahim Wakkala, wadanda suka ce suna mara wa wasu daga cikin manema takarar baya.

Wasu daga cikin masu neman takarar dai sun bayyana cewa sun shirya, kuma `yan kwamitin zaben kawai suke jira.

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi daya cikin masu neman takarar ya shaidawa BBC cewa yana fatan za a yi zaben da kowa zai yadda da shi.

Ya ce sun samu tabbaci daga rundunar 'yan sanda kan za su tabbatar da tsaro a wajen zaben.

Zaben fidda gwani a jihar Zamfara na jan hankali ne bayan da gwamnan jihar bai barin gado Abdul'aziz Yari Abubakar ya sanar da nuna goyon bayansa ga kwamishinansa na kudi Alhaji Mukthar Shehu Idris a matsayin wanda yake son ya gaje shi.

Wannan matakin ne kuma ya sa sauran 'yan takarar da suka kunshi har da mataimakin gwamna suka yi kokarin hade kai domin yakar zabin na gwamna Yari.

Zaben fitar da dan takarar gwamna na jam`iyyar APC a jihar dai yanzu ya raba kan kusoshin gwamnatin jihar, kasancewar gwamna da mataimakinsa sun yi hannun-riga.

Kuma duk da cewa `yan takarar suna da yawa, amma masu lura da al`amura na ganin cewa a karshe kokuwar za ta kare ne a tsakanin bangarori biyu, wato tsakanin zabin gwamna Abubakar Yari da madugun siyasa a jihar, Senata Sani Yariman Bakura, da kuma bangaren masu adawa da hakan.

Zaben dan takarar APC a Legas

Batun fidda dan takarar gwamnan APC a Legas na daya daga cikin rikicin jam'iyyar da ke jan hankali, kasancewar alamu da suka nuna uwayen jam'iyyar a jihar ba su goyon bayan gwamna mai ci.

Gabanin zaben fitar da gwanin, 'Yan takarar fidda gwanin na APC a Legas sun yi musayar kalamai masu zafi tare da kuma zargin juna.

A wani taron manema labarai a ranar Lahadi gwamnan jihar Legas Akinwunmi Ambode ya zargi Alhaji Babajide Sam-Oulu da cewa mutum ne da aka kama da laifin amfani da kudin jabu a Amurka har aka daure shi da kuma cewa ya taba samun tabin hankali.

Amma a martaninsa Alhaji Babajide ya kame bakinsa yana cewa shiru ma magana ce, yana mai cewa uwar jam'iyyar APC ce za ta mayar da martani.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sakamakon zaben Legas zai tantance tasirin Tinubu a siyasar jihar

Masu lura da al'amura dai na ganin sakamakon zaben fidda gwanin zai yi tasiri sosai ga makomar karfin uban jam'iyyar Bola Ahmed Tunibu idan har wanda yake mara wa baya ya yi nasara ko kuma sakamakon ya rage tasirinsa a siyasar jihar idan har Ambode ya yi nasara.

A martaninta, babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta ce kalaman Ambode sun tabbatar da cewa APC jam'iyya ce ta mayaudara da ke shirin yin magudin zabe.