Zaben fitar da gwani ba zai yiwu ba a Zamfara - Yari

Gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari
Image caption Gwamnan Zamfara ya ce ya tabbatar wa shugaba Buhari cewa zabe ba zai yiyu ba

Gwamnan jihar Zamfara ya yi barazanar cewa ba za a yi zaben fitar da gwani ba na APC a jiharsa har sai an bi ka'idar da suka sani.

An dai samu sabani ne tsakanin gwamantin jihar da kwamitin zabe a kan ka'idodjin zaben, ciki har da batun rajistar da za a yi amfani da ita wajen tantance masu zabe.

Gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari Abubakar ya yi watsi da tsarin zaben da kwamitin uwar jam'iyyar suka ce za su yi amfani da shi wanda ya ce ya saba ka'ida.

Kwamitin da uwar Jam'iyyar APC ta tura domin gudanar da zaben a Zamfara ya bukaci duk wadanda ke da kati a jihar su fito su yi zabe.

Gwamnan ya shaidawa BBC cewa ka'idar zaben da suka sani shi ne sai 'yan jam'iyya kuma wadanda sunayensu ke cikin kundin rijista za su yi zaben.

A cewar gwamnan tsarin da shugaban kwamitin zabe ya ce za a bi zai iya haddasa husuma a jihar, kuma gwamnatinsa ba za ta yarda ba.

"Maganar zabe zai yiwu kadai ne idan za a bi ka'ida idan kuma ba ka'ida babu zabe", in ji gwamnan na Zamfara.

Ya kuma ce ya tabbatar wa shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa zabe ba zai yiwu ba a jihar Zamfara har sai an bi ka'ida.

Gwamnan ya zargi 'yan kwamitin da yin gaban kansu ba tare da sun same shi ba a matsayinsa na jagoran APC a jihar.

Ya ce duk da ba shi ke takarar gwamna ba, ya kamata da suka isa jihar su same shi.

Jihar Zamfara dai na cikin jihohin APC da ke fama da rikicin cikin gida inda wasu 'ya'yan jam'iyyar suka ja daga da gwamnan jihar.

Zaben fidda dan takarar gwamna kuma ya ci tura bayan kwashe yini biyu ana kokarin gudanar da shi.

Rikicin siyasa a Zamfara ya kara zafi ne bayan da Gwamna Yari mai barin gado ya sanar da goyon bayansa ga kwamishinansa na Kudi, Kogunan Gusau Alhaji Muktar Shehu Idris, a matsayin wanda zai gaje shi.

Wannan ne ya sa wasu daga cikin masu sha'awar takarar gwamnan a jam'iyyar APC su takwas da suka hada da mataimakin gwamnan Ibrahim Wakalla da kuma Ministan tsaro Mansur Dan Ali suka hade kai domin yakar gwamnan na Zamfara.